Rahotanni daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na fama da 'yar gajeruwar rashin lafiya, kamar yadda majiyarmu ta Sahara Repoters da Premium Times suka rawaito a safiyar yau.
Bayanan sun nuna cewa shugaban kasan ya na fama ne da ciwon kunne. Wanda ake zargin cewa ciwon ne ya hana shi gudanar da ayyuka a cikin 'yan kwanakin nan, musamman wadanda suka shafi tafiye tafiye.
Likitoci na duba shugaban kasar ne a asibitin da ke fadar shugaban kasa.
Muna fatan Allah ya baiwa shugaba kasar lafiya, ya kuma sa kaffara ce.
Title :
Buhari Na Fama Da Gajeruwar Rashin Lafiya
Description : Rahotanni daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na fama da 'yar gajeruwar rashin lafiya, kamar yadda...
Rating :
5