A wani mataki na karyata ikirarin Boko Haram, gwamnatin Amurka ta fito fili ta tabbatar da cewa Boko Haram ba ta da wani hakikanin alaka da kungiyar ta'addancin nan ta IS wadda ta samo asali daga Iraq kuma ta yadu zuwa kasashen Siriya da Libya.
Ma'aikatar Harkokin wajen Amurka ta nuna cewa kungiyar Boko Haram ta yi wannan ikirarin ne a matsayin neman taimako a fakaice daga kungiyar ta IS inda ta yi nuni da cewa a kasar Libya ce kadai kungiyar ke da reshe a nahiyar Afrika.
A cewar ma'aikatar, a halin yanzu Amurka za ta mayar da hankali ne a Libya don ganin an murkushe ta'addancin kungiyar ta IS kafin ta fara yaduwa a kasashen Afrika.
Rariya
Title :
Babu Alaka Tsakanin Boko Haram Da Kungiyar IS - Amurka
Description : A wani mataki na karyata ikirarin Boko Haram, gwamnatin Amurka ta fito fili ta tabbatar da cewa Boko Haram ba ta da wani hakikanin alaka da...
Rating :
5