Wani bidiyo ya bullo a Indiya wanda ke nuna yadda aka tursasa wasu Musulmai biyu cin kashin shanu, bayan da 'yan kato da gora na addinin Hindu suka kamsu da naman shanu.
Kafar watsa labari ta kasar ta ce al'amarin ya faru ne a jihar Haryana, yayin da Musulman ke kan hanyarsu ta zuwa Delhi kai naman.
Wani dan kato da gora ya ce an sa mutanen ne a gaba aka kuma basu kashin shanun wanda aka cakuda da fitsari da madara, a cewarsa ''domin a koya musu hankali a kuma tsarkake su.''
Mabiya addinin Hindu dai na bautawa saniya, don haka ba sa so su ga ana cin namanta. An haramta yanka shanu da sayar da namansu a jihar Haryana, amma ba duka jihohin Indiya suka sa wannan haramci.
Title :
An Tursasa Musulmai Cin Kashin Shanu A Kasar India
Description : Wani bidiyo ya bullo a Indiya wanda ke nuna yadda aka tursasa wasu Musulmai biyu cin kashin shanu, bayan da 'yan kato da gora na addini...
Rating :
5