A yau ne, aka gurfanar da mutanen da ke da hannu wajen kisan 'year kabilar Igbo din nan, Misis Bridget Agbaheme a Kano bisa zarginta da laifin batunci ga Manzon Allah (SAW).
Wadanda ake zargin dai su biyar ne wanda ya hada da jagoransu, Dauda Ahmed, ana dai tuhumarsu ne da aikata laifuka har guda hudu wanda ya hada da kisan kai.
Mai shari'a a kotun, Abubakar Jibrin ya dage sauraren karar zuwa ranar 28 ga wannan wata bayan wadanda ake tuhumar sun ki amsa laifinsu.
( A kasa, hoton mutanen hudu ne da ake tuhuma a cikin kotu)
Title :
An Fara Shari'ar Wadanda Suka Kashe Misis Bridget A Kano
Description : A yau ne, aka gurfanar da mutanen da ke da hannu wajen kisan 'year kabilar Igbo din nan, Misis Bridget Agbaheme a Kano bisa zarginta da...
Rating :
5