.
Musti ya dan nisa kadan, ya juyo ya kalli Sani " Yanzu dai bisa ga dukkan alamu dole a sake lale, don na lura akwai baraka a wasu wuraren, ka san abin da Ust. Aliy ya ce min ne? Wai a fitowa sharan da muke yi, duk wanda aka sare shi ya mutu a cikinmu dan wuta ne, bábá wutannan fa sun ce ta fi ta duniya zafi, ka san ko ta sigari ce ta dan kuskure ka matsala ce, to bare ta lahira, ba na tsammanin wancan za ta yi daidai da ta sigari, ainihin wutar ce billahillazi"
.
Sani ya dan nisa kamar yana tunani, a qarshe ya juyo ya kalli Musti " Ka san abin da nake tunani ne? Ina ganin kamar ba ka ji da kyau ba ne, in har ka kai wani lahira ya kasance za ka shiga wuta, wannan ai kai waye ne ba matsala, amma wanda aka sabauta meye kuma na zuwa wuta? Ga kisa ga shiga wuta kuma?" Musti ya amsa masa da cewa "Ni ma abin ya daure min kai, amma wani da ya tambayi malamin, na ji ya ce Annabi ne ya fada, ka ga kuwa kat kenan, abu mafi mahimmanci kawai mutum ya sani ko shi ya kashe ko kashe shi aka yi duk dai wuta ce makoma, gwara ma in da sauran rai mutum ya fara istigfari ko zai rage na baya"
.
Gayu dai duk jiki ya yi sanyi, in ba don shedan ba kana iya cewa daga yau duk sun tuba kenan, don Sule ma a birkice yake, ya dubi Musti ya ce " To Garus da muke cewa ya yi shahada ma'ana ba aljannan ya je ba kenan? Ka san shi ma a gwarawar Karmata ne ya harba, Musti don Allah me dan Ustaz dinnan ya ce ne?" Musti ya fara magana yana dan dukar qasa da wata karyayyiyar sanda da ke hannunsa.
.
Ya dan yi shuru sannan ya ce "Cewa ya yi idan musulmai Biyu suka gwara da makamai to da wanda aka kashe da makashin duk suna wuta, ni gaskiya na fahimci cewa wanda ya kashe wani yana wuta, sai dai wanda aka kashe din ne ni ma ya daure min kai, don na kasa gano dalilin da zai kai shi wuta? Da aka matsa masa da tambaya ne ya ce Annabi SAW ya ce da mataccen ya sami dama, da shi ya kai makashinsa lahira, kai ma ka san wannan ko bai fadi ba haka yake, bare kuma Annabi ne ma ya fada"
.
Sun kusan kwashe minti goma ba wanda ya iya cewa uffan, can sai Sani ya yi gyaran murya ya ce " Don Allah ku daina kawo mana irin wannan, duk jikina ya yi sanyi wallahi, Musti ne ma da yake yana da dan imani sai zuba yake yi, bai ko ji a jikinsa ba" Sule ya sunkuyar da kai yana dariya "Ka ji maganar banza, Musti din da ya je gidan ta'aziyyar Garus yana ce musu wai su daina kuka tunda ya dace da shahada? Me kake gaya mana yanzu"
.
Sani ya dan yi murmushi yana ba shi amsa "Ai kuskure ya yi, na gaya masa tun da ya riga ya fita a hankalinsa da ya bari sai hankalinsa ya dawo kafin ya tafi, amma dan gogan na ka ya nace sai ya tafi, shi ya sa kawai na rabu da shi" Sule ya miqe ya zo gaban Sani yana magana yana dariya "Dan gogan na ka lilo yake ta yi ko tsayuwa bai iya yi, ya narki shalisho ya yi tab, amma haka ya je wajen Ustazannan yana ce musu: Yanzu da kuke mana kallon qasqanci me za ku ce wa Ubangiji? Ga Garus nan ya yi mutuwar shahada, na san da wahala dayanku ya sami shahada irin ta sa, ga limamin gari a zaune!"
.
Suka bushe da dariya, Musti ya dan yi murmushi ya kawar da kai, Sani ya ce "Au ko dalilin da ya sa Ustaz Aliy ya kira shi kenan ya saka masa karatun malam Jafar?" Duk suka yi shuru, ba dai wanda ya ce uffan a cikinsu, ko shi Musti din ya san ya buga, don 'yan uwansa sun yi ta yi masa fada lokacin da ya dawo hayacinsa.
.
Zuwa dan anjima kadan Sani ya ce "Ko ma dai mene ne akwai gyara, na yi wani dogon lissafi ta ko'ina na fahimci cewa mutum yana da buqatar sake duba kansa, domin yadda ake mutuwa a 'yan tsakaninnan dole mu dan gyara kar mutum ya yi wa duniya zuwan kifi, in ba bom ba, to boko haram, in ka samu ka tsallake wanan ga masu tsare hanya, kuma na ji an ce Burutai ya ce za su sanya qafar wando daya da duk wanda ya sake tsare wa 'yan qasa hanya"
.
Musti ya buda wa Sule ya zauna sannan ya ce " Gaskiya jama'a suna ganin laifimmu ne, amma mu ma ai muna da ranarmu in ka lura, kalli dai sabon masallacin Mandawa yadda dattawannan suna gani aka zuba wa gayu ICD a cikin farau-farau to tir ba wanda ya yi, ka ga ai bai dace ba, tunda kowa ya san qwaya ce" Sule ya karbe "Ai kuwa ita ma qwaya ce gaskiya, don takan sa a ji garau"
.
Sani ya gyara kwalar rigarsa ya dada tsayar da ita sosai ya ce "Kun kuwa san cewa dattawannan daga baya su ma sun sha PR?" "Haba dai! Kamar ya?" In ji Sule, Sani ya ce "Ai da aka gano su, su ma dandaqa PR aka yi aka watsa a kununsu aka ce wannan na manya ne kar a taba, ai da suka sha suka yi daidai sai kowa ya dauki kwangiri jikinsa yana rawa, sai ji kake suna cewa : Ai aljanna ba ta matasa ne kadai ba, wallahi da su aka qare aikin, sai dai kuma kashe gari ba wanda ya leqo a cikinsu"
.
Suka qyalqyale da dariya, sannan Musti ya ce "Ina ganin bai kamata a riqa haka ba tunda mun san darajar manyanmu, koda yake suma sun dan yi laifi, ya kamata su tsawatar ne don sun fi kowa sanin aibinta, yanzu dai ni na yi wa kaina fada in Allah ya yarda na dena wadannan abubuwan, mun ma shirya da Ustaz Aliy zan fara koyon baqi gobe, ya ce kar na ji komai, duk abin da nake so zai nuna min, fatata dai Allah ya taimake ni kan abin da na yi niyya, don duk inda mutum ya kai ga iskancinsa akwai wanda ya dama shi ya shanye, qarshe mai kyau na mai tsoron Allah ne"
Daga Muhammad Alkasim