safiyya ta taka gaba daga inda take tsaye tare da cewa "nasan sadaukarwa irin wannan nada wuyar gaske sbd na dade da sanin yadda kikai zurfi a son Abbas tunda dadewa, amma kiyi duba da cewa shi kuma bake yake so ba.
Nasan Abbas ma2ka idan aka tilasta masa za'a iya samun matsala wallahi!!"
takai karshen maganar dai-dai sanda ta zauna tana me duban zahra.
Zahrar tabita da kll tare da cewa "matsala?? Ke kike ganin haka amma ni ko kadan bana gano hkn, tayaya ma wacce zcyrta ta ginu akan syy za'a tunkareta da batun sadaukarwa??
Hakan bame yiwuwa bane."
da sauri safiyya tace "amma......"
zahra ta katseta da cewa "kada ma ki bata bakinki sbd bazan iya ba."
Duk iya kokarin da tayi abin yaci tura haka ta hakura.
** kwana a tashi kwanakin sai kara tahowa suke kmr wasa kuma zancen sai kara karfi yake, tun abbas na daukar zancen sa ranar aurensa da zahra da wasa har takai shi da kansa ya yarda tbbs da gaske ne.
Yayi korafi iya iyawarsa amma a banza, sanda ya rage kwanaki uku kacal asa ranar ne (sa ranar tazo dai-dai da ranar da abbas yayiwa maryama alkawarin mayar da ita ga iyayenta) yayi ta amsar wayoyi daga ko'ina akan fatan alheri da ake masa.
Wasu ma na zolayarsa wai yaki gaya musu sai dai suji a bakin duniya wanda hakan ya faru ne sakamakon katinan da suka baza gari masu dauke da nunin da murnar engagement da za'ai ranar asabar 14-6-2014.
Na BARRISTER ABBAS ABDULMUMIN da ZAHRA USMAN SADA.
Party na musamman a tropicana hotel a daren asabar din misalin karfe 7:00 manyan baki kuwa ba'a magana, shirye-shirye ake kai kace lkcn daura auren ne ma ya taho.
Imran ne keta kaiwa da kawowa akan batun bisa umarnin daddy shine ya sanar da dukkan abokansu akan auren abbas din, wadanda keta kiran abbas din suna yi fatan alheri.
Duk wanda ya tambaya "waye ya gaya ma zanyi aure??"
sai su bada amsa da IMRAN.
Shi yasa har ya fara jin haushinsa ma.
*yayinda ya rage kwanaki biyu (ranar alhamis kenan) imran ne a ckn motarsa shi kadai misalin karfe uku na rana byn ya fito daga ofis kasancewar yau da wuri ya fito, ckn sauri yake tuka motar kai da gani kasan inda ya dosa yake son ya isa akan kari.
Mikewa, kwane-kwane gami lankwashe-lankwashe har ya iso inda yake da burin zuwan, da mamaki zuwansa gdn marayu a karona biyu tun byn zuwan da suka tabayi sau daya tak da Abbas shekaru 3 da suka gabata.
Da alama musamman don maryama yazo dauke da babban sako da yake bukatar ta sani ckn gaggawa, kai tsaye ciki yayi da motar bai dakata ba har sai daya iso inda ya tbbtr zai sameta sannan yayi parking tare da fitowa ya jingina a jikin motar tashi yana me bin dai-dai kun yaran dake giftawa lkc zuwa lkc.
Sautin karatun yara ne kawai ke tashi daga tsirarun azuzuwan gdn, bai wani jima a tsaye ba sannan wani dan matashin yaro yazo giftawa, "kai! Zo."
imran ya fada. Yaron ya tako da sauri izuwa gabansa yace "gani".
Imran ya dan juya gami da klln sassan ilahirin gdn ya dawo da dubansa ga yaron yace "maryama nake nema kuma nazo ban ganta ba ina ta tafi??"
tana aji tana koyar da karatu.
Yaron ya amsa.
Allah sarki!! Imran ya fada tare da cewa "to don Allah jeka kace mata imran ne ke son ganinta kaji!!"
yaron ya grgz kai tare da cewa "aunty bata kula kowa idan ba uncle Abbas ba."
dariya tadan kwacewa imran yace "idan kace mata imran ne zata zo kaji? Yi maza."
yaron ya gyada kai tare da juyawa ya nufi daya daga ckn azuzuwan dake nesa kadan da inda yake tsaye. Jim kadan ta fito ckn cikakkiyar shigarta ta kamala data saba, sai data hanga izuwa wani sashe daban sannan ta juyo ga sashin da yake, hangoshi da tayi yasa tayo inda yake tsaye.
Da murmushinta tace "da mamaki! Kaine da kanka??."
nasan zakiyi mamakin dama, nine. ina mutumin nawa kuma??
Ta sake tambaya.
Imran ya grgz kai tare da cewa "ba tare muka zo ba, ni kadai ne kuma nazo ne na sanar dake cewa Abbas din ma da yake zuwa gaf kike da daina ganinsa har abada."
a hnkl fuskar murmushinta ta fara murtikewa ta bishi da klln rashin fahimta kawai.
Ya taka gaba kadan tare da cewa "nasan bai zama lallai ya gaya miki ba shi yasa ni na dauki alhakin na fada miki, jibi asabar za'a saka ranar bikin Abbas da wata amma bake ba."
da sauri kafarta ta dama tayi baya sbd grgz, idanunta suka fito waje kmr zasu fado ba tare da furta komai ba ta cgb da binsa da kll kawai.
Ya tako gami da giftawa ta gabanta yana cewa "nasan cewa zakiji zafin hakan amma kiyi hakuri shine gskyr abnd yake faruwa a halin yanzu, ki cire rai daga batun abbas sbd aurenku dashi abune da bature ke kira IMPOSSIBLE.
Ya tako da baya tare da cewa "koda cewa ke kanki kinsan dama Abbas ba tsararki bane ta kowanne bangare, ki dauka cewa kun danyi abota ne ta wani lkc amma ynz kun rabu na har abada."
ckn muryarta da tayi sanyi ma2ka tayi karfin halin cewa "banyi zaton kana daga ckn masu yada jita-jita ba kmr yadda nayi mamakin nuna bakin cikinka da syyrmu da Abbas a fili da kayi, hakan yasa bazanji kunyar cewa karya kake yiba."
ta fada idanunta kuru-kuru akansa.
Yayi guntun murmushi tare da cewa "tbbs ina bakin ckn ace abokina me ckkn asali ya rasa wadda zai aura sai ke, kuma baki isa nayi miki karya ba, Abbas ya samu wacce tafi ki komai da komai, kuma wacce babu tawaya a asalinta."
ya zaro katina da yawa a aljihunsa ya watsa mata gami da cewa "na engagement ne kuma muna gyytrki party na musamman a ROYAL TROPICANA idan zaki zo sai kuyi bankwana ma acan."
ya kyalkyale da dry ya taka da baya ya shige motarsa, dai-dai lkcnne hwy tamkar an finciko su suka zubo daga idanunta.
Tabi motar tashi da kll ko kiftawa bata yi.
Wayyo ''SO'' taya abbasa ze wanke kanshi akan wannan har gitsatsen lamari..???
Kubiyoni danjin yadda al'amarin xe na kasancewa...!