BYN KWANAKI UKU*
Misalin karfe 6:00 na yammaci Tun daga harabar gdn ma'aikatan gdn ke musu barka da dawowa, safiyya na jaye da jakar kll zakayi musu kasan dukkaninsu a gajiye suke.
Kai! Gsky na gaji da yawa! Safiyya ta fada. Abbas ba tare daya kllta ba yace "kema kenan ina kuma gani??"
ba tare da sun kara cewa juna komai ba suka nufi hnyr shigewa ckn gdn, cak! Momi dinsu ta mike gami da amsa sllmr tasu byn da suka shigo.
Mutanen karkara an dawo??
Ta fada fskrta fadade da murmushi.
Mun dawo momi, Safiyya ta fada.
Dai-dai lkcnne daddy ya shigo yana kokari zama, ya dubesu tare da cewa "lallai na lura kauyen nan ya muku dadi, kllsu hjy har wani fari suka kara."
yakai karshen maganar yana dubanta.
Abbas da safiyya suka dubi juna gami da yin dariya abbas din ya kada kai yace "kodai mun kode? Gsky karkara ba dadi wlh."
duk sukai dariya, momi tace "koba komai dai an sada zumunci."
daddy ya dubi safiyya tare da cewa "kin fada musu sakon??"
ta gyada kai tare da cewa "na fada musu daddy baka ga farin cikin da sukai ba sunce bama sai kaje ba zasu taho ranar alhamis ta sama kaga kwana biyu kafin ranar engagement din kenan."
da naso ace... Shikenan dai sai sunzo kafin nan muma duk mun gama shirye-shiryenmu Hakan yayi. Ckn rashin fahimta Abbas yace "wai sa ranar wa??"
daddy ya canja fuska tare da cewa "taka kaida zahra nan da kwanaki goma masu zuwa, an sanar da y'an uwanka shine dlln tfyrku wannan kauyen.
Tuni Na fara shirye-shirye yadda za'a aiwatar da abubuwan sai ka zama ckn shiri sbd tun a bikin sa ranar aurenku duniya zata fahimci cewa auren na Y'AY'AN GATA ne, kafin zuwan babban bikin wanda kowa sai yasan za'a yishi a kasar nan."
Idanun Abbas suka zaro fskrsa ta canja yabi dukkaninsu da kll daya byn daya sannan yace "to wlh dana san haka ne kauyen ma bzn je ba, na tafi da karfin gwiwata da nufin zumunci ashe ban sani ba shirye-shiryen rusani ake yi??"
ya fada gami da binsu da kll yayiwa safiyya wani kll me kama da harara ya dauke kai tare da takawa yabar falon, daddy yabishi da kll tare da cewa "wai me yake damun wannan yaron ne??"
kuruciya mana, duk sanda irin wannan zai faru ai ba'a rasa dan tirjiya irin wannan amma kasan ai dole ma ya hkr ko??
Momi ta fada.
*tunda ya shige dakin yana rufewa ya daki kofar cike da haushi gami da jan tsaki, tsaye yayi kyam! Kmr me tunanin mafita zuwa can ya kara jan dogon tsaki ya taka izuwa cikin dakin.
Tun daga sannan ko sha'awar ya fito falon ma bai kara yi ba, byn awanni biyu yana kishingide madaidaiciyar laptop na gabansa yana sarrafawa.
A hnkl kofar dakin nasa ta bude safiyya ta shigo hnnta rike da wani faffadan babban faranti wanda ke dauke da plask din abnc gami da kananan plates dake zagaye dashi, tayi sallama tare da tsayuwa a kansa sai daya amsa sallamar sannan ta ajiye.
Ta zauna a gefen gadon tare da cewa "brother".
Sister!!
Ya amsa mata kansa nakan abnd yake yi lkc guda kuma ya dago kai.
Naga kama ki fitowa bare ka nemi abnc shi yasa na biyo ka dashi, sbd kadan ne daga aikinka kace zaka kwana da yunwa.
Ta fada.
Ya gyada kai tare da cewa "kwana da yunwa shi yafi min sauki akan abnd ake so ayi min."
kmr bata fahimci abnd yace ba tace "kmr yaya??"
kinfi kowa sanin abnd nake nufi ai, wato har dake za'a hada baki ayi min auren dole ko??
Ya fada gami da tsare ta da ido.
Ta kasa rike dariyarta har sai data fito fili, tace "brother ba haka bane, umarni aka bani kuma na isar dashi kuma nima zanyi farin ciki idan hakan ya faru, yaya wlh kun dace da zahra ma2ka kuma ni banga aibunta ba shi yasa nake mamakinka.
Kuma abnd baka sani ba zahra ta dade tana kaunarka kaine dai baka san haka ba."
Abbas ya tashi zaune sosai yace "idan tana sona ni kuma bana sonta, shi kuma aure ba'a gina shi akan SO DA KIYAYYA.
ana ginashi ne akan SO DA SO kmr yadda mukewa juna ni da maryama."
maryama! Maryama!! Wai wacece maryaman nan ne dakayi nisa a ZAFIN SOnta haka??.
Safiyya ta tambaya.
Abbas yace "itace wacce nake so, wacce nake fata kuma bana jin zan iya auren wata idan ba ita ba, a gdn marayu ta taso kuma ta girma sai dai abin mamaki a ynz an samu iyayenta na ainihi wanda hkn yazo akan gabar daya dace.
Kusan shekaru hudu kenan da haduwarmu, ta yarda dani ta gasgatani kuma dukkan karfin gwiwarta akaina yake, bata da wani fata da kyakykyawan zato idan ba daga gareni ba.
Sai naje na gaya mata na fasa aurenta y'ar uwata zan aura, na mata adalci??"
safiyya tayi shiru kmr zata ce wani abu amma ta fasa, ta dubeshi tare da cewa "ynz dai ga abncnka nan ka tashi kaci nasan yunwa kake ji."
takai karshen maganar sanda ta mike tsaye.
To zanci.
Ya fada kawai tare da mayar da kansa ga laptop din dake gabansa.
Don Allah! Kada in tafi kaki ci!! Ta fada tana dubansa.
Ya dago kai tare da dubansa yace "idan bzn ci ba zan gaya miki ki dauke kayanki ai, ko tsoronki nake ji??"
ta tuntsire da dariya kawai ta nufi waje.
*Zahra ce zaune bisa gado daga can saman fuskarsa ba wani aiki take ba, ba barci ba, amma kyam take ko motsi batayi wanda ke nuni da zurfin da tayi a tunani.
Har sai da safiyya ta taba ta sannan tayi firgigit byn da tayi mata sallama batama san tayi ba, tunanin me kike??
Safiyya ta tmby.
Zahra tayi murmushi tace "rywr aurenmu da abbas nake hangowa.."
safiyya ta katseta tare da cewa "kada 2naninki ya baki cewa akwai wani alfanu a ciki sbd yaya abbas bake yake so ba, bana jin kuma hkn ya zame muku alkhairi.
Mezai hana ki sadaukar da syyrki ga wacce yake so??
Sbd a halin yanzu ke kadai ce zaki iya warware wannan matsalar, na tbbta da zarar kince bakya sonsa dole a hkr."
uhmm batasan meye so ba shisa take wannan tunanin....
Kasance da mu akodayaushe dan JOining din mu ko kuma
Like
Title :
Zafin So Part 7
Description : BYN KWANAKI UKU* Misalin karfe 6:00 na yammaci Tun daga harabar gdn ma'aikatan gdn ke musu barka da dawowa, safiyya na jaye da jakar...
Rating :
5