*kinsan dai yayana ba haka yake ba ko?? Bake ba ko almajiri yana da darajar da bazai wulakantashi ba bare ke.
Zahra ta mayar da kanta tare da cewa "Allah ya
baki hkr amma dai kinsan duk yau haushina yake ji, na rasa dlln da yasa yaketa hararata." manta dashi.
Safiyya ta ta fada tare da kara takowa inda take
tana me cewa "ynz dai wlh shine da kansa yace a kiraki da alama ya sakko ya hkr ne..."
bana tunanin haka. Zahra ta fada.
Safiyya tabita da kll tare da cewa "koma dai meye yana kasa yana jiranki, kisan yadda zakiyi ki fara
ginawa kanki foundation a zcyrsa wannan itace
damarki ta farko.
Zahra ta saki murmushi tare da cewa "zanyi iya
kokarina don ganin na samu zcyr dana dade ina
neman inda take yanzu kuma na ganta dole na farauceta da dukkan karfina."
ta mike tare da jawo mayafinta ta yafa tare da
takawa, safiyya ta jinjina mata tare da cewa "kin
gama haduwa amma ki gyara tafiyarki."
zahra ta harareta kawai kai tsaye tayi waje.
¤zaune yake bisa farar kujera a harabar wurin me dauke da daddadar iska dake kadawa, idanunsa na kan faffadar wayarsa yasa wani dan karamin tebiri a gaba wanda shine ya shiga tsakaninsa da kujerar dake fuskantarsa.
Da sallamarta ta iso ta zauna a kujerar, idonta na kansa."
sai da wasu y'an sakwanni suka shude sannan ya amsa sallamar tare da dago kansa, suna hada ido ta kara sakin murmushi yayi sauri ya dauke kansa kmr bisan tanayi ba Zuwa can ya gyara zama tare da cewa "sannu da
fitowa."
wani sanyi ya dira a ranta sbd dadin abnd ya fada tace "yauwa sannu da hutawa yayana.."
bata karasa ba yace "nasan kinji abnd su daddy
suka ce wanda ni dake duk bamuyi zaton haka ba, sbd babu wata magana ta syy a tsakaninmu.
Maganata gsky ni banji dadin haka ba sbd hankalina ba'a kanki yake ba ina da wacce nake so kuma nayi mata alkawarin aure, kmr yadda kema nasan bani kike so ba??"
da sauri zahra ta grgz kai sannan tace "karkayi
tunanin haka, idan nace bana sonka nayi karya
magana ta gsky na dade ina kaunarka ina burin ka zamo mijina.."
bai san sanda ya zabga mata harara ba tare da
cewa "ba ruwana da wannan abnd nake so na
sanar dake shine nifa ban taba ji a raina ina miki
son dazan iya aurenki ba, don ki taimaki kanki
muyi hnyr da zamu rabu ta ckn sauki. Zanyi iya kokarina don naga nasa an tambayeki
shin kina sona??
Ina so ki bada amsar bakya sona bakya kaunata
sai dai idan dole za'ai miki."
zahra ta dago kanta tare da cewa "hkn shine mafi kokoluwar yaudarar da zanyiwa kaina, a ko'ina kuma a gaban kowa zan fada cewa kaine nake so bani da shakku akan haka.
Abbas ya dauke kansa sbd haushin data bashi
zuwa can ya dawo da kansa garesu sosai
hannunsa biyu na dafe da tebirin dake gabansa
yace "ana so dole ne??" zahra ta dubeshi sosai tace "za'a fara yanzu."
ya maida kansa tare da cewa "kada kiyi tsammanin wai rokonki nakeyi sbd hknne kawai abnd zan iya yi, wlh nafi karfin a tilastani kema kinsan haka."
Sau da yawa kakan ki abu da farko kuma daga
baya ya zame maka alkhairi, abnd nake fatan tarayya fatan zai faru a tarayyarmu kenan.
Zahra takai karshen maganar sanda ta dubeshi.
Kansa na jikin kujerar yace "kanki zaki cuta kuma
kada kiga laifina akan duk abnd ya faru."
babu cutar kai a ckn syyrka sbd na tbbtr kai ba
azzalumi bane kuma ba zaka zama akaina ba." yaja dan gajeren tsaki ya kauda kai, duk dabarun da yake 2nanin zaiyi amfani dasu yayi amma basuyi tasiri ba lallai ma wannan zahrar yaushe ta zama haka??
Ya tambayi kansa kmr zai ce wani abu kuma ya fasa lkc guda ya mike tare da gyara zaman faffadan glass dake idonsa ya zira takalmi gami da binta da kll bai ce komai ba ya juya yabar wurin.
Dafe kujerar da take kai tayi ta baya tafi
kyakykyawar salon tfyrsa da kll murmushi na tashi a fuskarta koba komai wannan ne karon farko data samu damar yin magana me tsayi da masoyin nata kuma ta iya amayar da abnd ke ranta, bata dade a wurin ba ta mike tare da komawa izuwa ckn gd.
** kmr yadda daddy ya fada musu washe gari
Abbas da safiyya shirin tfy kauye sukai, misalin
karfe 9:00 na safe tsaye suke suke su biyu ckn
shirin tfyr safiyya na rike da jakarsu a hannunta.
Daddy ne tsaye ya dafa Abbas tare da cewa "sai
kun dawo my son amma fa kada zaman yayi maka dadi ku zauna kwanaki da yawa kasan akwai ayyuka da yawa da zakayi a satin nan."
ba zamu dade ba daddy kauye ma ina yaga wani
dadin da za'a zauna kwanaki da yawa??"
momi dake zaune tace "kaji ja'iri asalinka ne dai
tunda har yanzu kakanninka suna can dai.." daddy yace "yauwa safiyya kada ki manta ki
fadawa kakar taku batun auren Abbas da zahra
sati me zuwa za'a sa rana, ki fada mata nima ina gaf da zuwa."
to daddy zan fada mata insha-allahu.
Safiyya ta fada. abbas ya bata rai tare da cewa "daddy don Allah abar wannan maganar, nifa ina da wadda nake so kuma na dade dayi mata alkawarin aure idan nayi mata haka zai zama na yaudareta kenan.
Kuma fa itama zahra ba ba sona take ba tana da
wanda take so bashi da wani amfani ace za'a tilasta mu."
daddy baice komai ba ya dubi safiyya tare da cewa "ke! Jeki kira min zahra ce tazo."
ta saki jakar dake hnnta tare da komawa da baya
izuwa dakinsu.
Jim kadan suka fito tare zahra ta durkusa da fadin gani daddy, yace "kmr yadda na fada akwai
alkawarin aure tsakaninku da Abbas tun tuni kin
amince kina sonsa??"
ta dago tare da duban Abbas tare da sunkuyar da
kanta tace "Daddy a baya ban taba kawo haka ba
shi yasa bana jin son yaya Abbas da aure, amma daga ranar daka ambaceshi a matsayin mijin da zan
aura sai naji nafi kaunarsa fiye da kowa a duniya."
Abbas ya zabga mata wata irin harara kmr zai
rufeta da duka sbd yadda takai makura wajen
bashi haushi, ya kauda kansa daga kllnta kawai.
Daddy yace "to kaji, idan har ita zata yi hkn sai kaine zaka bijire?? Baka taba bani haushi ba kada
hkn ya faru a wannan karon, sai kun dawo."
ya fada sanda ya wuce.
Mu tafi.
Abbas ya fada sanda ya dubi safiyya. Taja doguwar
jakar dake hnnta tare da duban momi tace "sai mun dawo."
to sai kun dawo, Allah ya tsare.
Ta fada.
Ameen suka amsa tare da yin waje, safiyya na
dagawa zahra hannu.
Suna fitowa wajen motoci suka nufa cak! Kuma safiyya ta tsaya tare da cewa "yaya nayi mantuwa
wlh, don Allah barina koma ina zuwa."
zaki bata mana lkc kuma kiyi sauri don Allah.
Ya fada sanda ya karbi jakar dake hnnta ya taka
izuwa motar yayinda da sauri ita kuma ta juya.
Zama yayi a kujerar gaban ba tare daya rufe kofar ba ya ziro kafafunsa waje, wayarsa ya dakko ya
kira maryama suka dan taba hira na y'an mintuna
yana kashe wayar safiyya ta dawo.
Yauwa mu tafi ko??
Ta fada sanda ta bude kofar gefen dama ta shiga,
abbas ya mayar da kafarsa cikin motar yaja kofar ya rufe dai-dai lkcnne safiyya tace "sanda muka fito
ranka a bace ka hade rai amma ynz na sameka ckn
walwala me yasa??"
da masoyiyata nayi waya mukayi hira..
Kafin ya karsa tace "kana nufin ZAHRA??"
wannan sunanta MARYAMA sarauniya a fadar koli kenan, wace wata zahra??"
yaja tsaki gami da tayar da motar ya fice daga gdn,
yadau doguwar kwaltar datai yamma don tunkarar
tfyr da zasu shafe awanni uku suna yi.
Title :
Zafin So Part 6
Description : *kinsan dai yayana ba haka yake ba ko?? Bake ba ko almajiri yana da darajar da bazai wulakantashi ba bare ke. Zahra ta mayar da kanta ta...
Rating :
5