*Ita kuwa maryama bin motarsa kawai tayi da kll har sai data daina hangota.
Wani murmushine ke tashi daga fuskarta ta dawo da kllnta ga wayar dake hnnta ta juya tare da barin wurin da take tsaye cike da farin cikin data dade batayi irinsa ba.
**BAYAN KWANA UKU**
Misalin karfe takwas na dare zaune a falon kayataccen gdn ahalin gdn ne dukkaninsu harda imran idan ka cire zahra wacce ita kadai ce bata falon, zaune a kujeru daban-daban. hira suke tabawa sosai, Abbas na bada lbrn a irin ynyn daya tsinci kansa a kasar germany da yadda zamansa ya kasance.
Zuwa daddy ya gyara zama tare da duban Abbas sosai yace "nayi iya iyawata dakai akan kayi karatunka a fannin kasuwanci amma kaki ka dage akan cewa lallai lawyer kake sha'awa, to gashi dai ka zama a yanzu.."
Abbas yace "daddy da ace ni kadai ne toda bani da zabi dole nayi kasuwanci amma akwai imran shima danka ne kuma abnd yake sha'awa kenan shi yasa naga toni bari na tafi wani bangaren.."
imran ya katseshi da cewa "daddy wlh ba wani fada kawai yake, fakewa kawai zaiyi da haka."
Abbas ya zabga masa harara kawai ya kauda kansa da cewa "Eh meye aibu don nayi kokarin yin abnd nake so??"
Daddy yace "koma dai meye yanzu gashi ka samu ai, ma'aikatar shari'a ta kasa ta nemi yiwuwar kayi aiki dasu to matsalar gsky dole sai dai ka koma Abuja da zama din-din-din to na nuna musu hakan bame yiwuwa bane.
Akwai ire-iren hakan da yawa amma gsky duk ban aminta dasu ba sbd wasu dalilai, daga karshe dai hukumar kare hakkin dan adam da kula da hakkokin mata ta duniya sun nemi kayi aiki dasu ta reshensu dake nan kano zaku zauna dasu zaka sa musu hannu a contract din da kukayi dasu, sannan ka shirya zaka fara lecturing akan shari'a a sabuwar jami'ar northwest university a ranakun karshen mako. Haka kuma an zabe ka a matsayin me lura da daidaiton tfyr da kotun ma'aikata ta kasa.
Don haka sai ka shirya ayyukan dake gbnka ba kanana bane."
Abbas ya gyada kai tare da cewa "insha Allahu zanyi iya bakin kokarina."
momi ta kada kai tare da cewa "aiki ya samu maza sai a mayar da hnkl ayi aiki tukuru da gsky kuma."
Abbas yace "momi dama ai ni banyi sha'awar yin wannan aikin don kudi ko abnd zan samu ba sbd ba sune matsalata ba, zanyi ne don Allah sbd sau da yawa me gsky kan zama mara gsky, mara gsky kuma ya zama me gsky sbd kudi.
Akan daure wanda bai cancanci dauri ba sbd watakila bashi da masu tsaya masa.
A wasu lktn kuma akan saki wanda yakamata a daureshi sbd kawai watakila yana da kudi da dama gami da kwararrun lauyoyin da zasu kareshi, wanda ba haka yakamata tsarin ya tafi ba."
daddy ya kada kai tare da cewa "na dade da fahimtar manufarka my son, ahh! Akwai mota ta zamani wacce aka yita musamman sbd mutane masu tfy daga wuri zuwa wuri nan da nan, takanyi tfyr awanni masu yawa ckn kankanin lkc nasa a kawo maka ita daga japan sbd yawan zirga-zirgar da zaka fara yi."
cikin rusunawa abbas yace "ina ma2kar godiya daddy Allah ya kara arziki da wadata."
ameen daddy ya fada.
Safiyya dake zaune can gefe tace "yaya duk ranar da zaka fara shiga kotu zamu je tare sbd ina so na ganka a ckn kayan lauyoyin nan kana zuba."
duk sukai dry.
Daddy yace "ka shirya kuma jibi asabar kenan? Zaku je can kauye kai da y'ar uwarka ku gaida mutanen can musamman kakar taku don kai wajen shekararka hudu kenan rabon dasu ganka, sai ka sanar musu da batun aurenka da kanka."
ckn rashin fahimta ya dago kai tare da cewa "aurena kuma daddy??"
hade da daga kai daddy yace "Eh aurenka da zahra, tsohon alkawari tunda dadewa kune dai baku sani ba."
wai zahra ta gdn nan??
Bakinsa na rawa ya tmby. "Kwarai ita" momi ta fada.
A hnkl fuskar Abbas ta fara sauyawa daga walwalar da take yi a baya, idanunsa suka zaro waje, zahra!! Ya tmby kansa.
Yabi fuskokin duk wadanda ke zaune a falon gami da zahra dake isowa falon a dai-dai yanzu, jin abnd aka fada yasa taji tamkar anyi mata albishir da aljanna, yau dai Allah ya kawo ranar da burinta zai dau hnyr cika.
Abbas kuwa juyowa yayi tare da cewa " amma ni gsky babu wani syy tsakanina da zahra domin ni ina da wadda nake so amma ba zahra ba."
zuciyar zahra ta buga da karfi kamar zata fito waje, lkc guda jikinta yayi mata wani yarrr! Dakyar ta iya zaman da take shirin bayanda hawayen zazzafan so suka riga dira kasa kafin ta zauna, da sauri da goge idonta ba tare da kowa ya lura ba.
Daddy yace "kana da wata ko babu kana sonta ko baka sonta duk bai shafeni ba kadai bi abnd nace maka don bama lallai ne ka fara aiki kafin a daura auren nan ba don haka ka zama ckn shiri" kafin Abbas yace komai daddy ya mike ya nufi sashensa.
Abbas ya kauda kai kawai fuskarsa a hade, momi tace "to meye abin bata ran?? Sai kace wani abin tashin hnkl??"
yana me karkada kai yace "momi kawai ni ba'a san ya nake ciki ba ba shawara kawai a yanke abu, ni kuma akwai wacce nayiwa Alkawari hakan sai ya zama na yaudareta kinga ban mata adalci ba."
ya mayar da kansa izuwa klln baya zuwa can ya juyo yabi zahra da kll ya dauke kai ya mike da sauri yabar falon.
Imran yace "kinji banza!, ya mike yabi bayansa." momi taja tsaki tare da mikewa itama, tana barin falon sautin kukan zahra ya fito fili.
Safiyya tayi saurin rufe bakinta tare da cewa "lfy? Meye haka??"
zahrar ta banbare hnnta daga bakinta da sheshsheka tace "na shafe tsawon lkt ina rainon sonsa a zcyt, har izuwa yau da Allah ya kawo dama dazanci moriya ashe wahalar banza ma nake.."
safiyya tace "ke rabu dashi dallah munafunci ne kawai amma yana sonki.." zahra ta grgz kai tace "kada kiyi karya sbd abnd yake fada har zcyrsa haka ne tbbs da gaske yake."
to idan ma da gaske yake ke baki ji kunyar yin kuka ba don Allah??
Gsky kin bada mata wlh, mtsss.
Safiyya takai karshen maganar da tsaki.
Zahra tace "idan da ace ke kike jin abnd nake ji na tbbt ba zaki ce.. Haka ba." safiyya tace "naji amma dai ki rage ZAFIN SO akansa idan kuma kika bari ya fuskanci haka zaki sha bakar wahala." zahra bata ce komai ba ta mayar da kanta ga kujerar cike da takaici.
Abbas na shiga dakin ya kara daure fuska, dakyar ya iya zama a gefen gadonsa, na auri zahra??
Ya sake tambayar kansa.
Idan hakan ya tbbt ya kuma zaiyi da MARYAMA wacce ta dauki duk yarda da karfin gwiwarta ta dora a kansa??"
bai dawo daga tunanin nasa ba imran daya shigo ya katseshi da cewa "meye haka wai? An taimakeka amma ko gdy bakayi ba??"
an taimakeni? Ko kuma ana nema a cutar dani??"
karya kake wlh taimakonka akai za'ayi maka aure a sanda ya dace kuma da wacce ta dace, gsky su daddy sunsan abnd ya dace dakai."
abbas yaja dogon tsaki tare da cewa "a zatona ba murna yakamata kayi ba jajantamin zakayi sbd ana nema a rabani da farin cikin rywt a bani wata daban.."
imran ya grgz kai tare da cewa "cewa zakai an rabaka da wacce bata dace dakai ba kuma bata cancanci zama da mutum kmrka ba."
maryamar?? Abbas ya tmby. Imran yace "ita din, yakamata ka farka daga mafarkin wata maryama a rywrka ka fara mafarkin fatimatuz-zahra'u matarka bada dadewa ba kenan."
ya kyalkyale da dariya yayi waje.
Mtss.. Kaji banza!! Abbas ya fada sanda yabi gadon ya kwanta.
*tun daga lkcn ya rasa abnd ke masa dadi dai-dai da barci kasawa yin me dadi yayi a ranar domin ya tbbtr maganar da gaske ake, ya zaiyi??
Meye mafita a gareshi?? Abnd yaketa tunani kenan tsawon lkc.
Ko washe gari wajen breakfast ba'a ckn walwala yake kmr yadda ya saba ba banda haushin zahra kuru-kuru a fuskarsa suka zauna, ranar kuwa yini yayi yana harararta bai taba jin yana nema ya tsaneta ba sai a yanzu.
¤¤misalin karfe 5.00 na yammacin ranar zahra ce zaune bisa kujerar dake fuskantar faffadan mudubin dakin nasu tasa kayan kwalliya a gaba, tana tayi.
Kyakykyawar shigar farin leshi tayi tayi wadda ta ma2kar yi mata kyau, bayan data gama dandasa kwalliyar data fito da cikakken kwarjinin fuskarta.
Tana ckn daura dan kwali ne safiyya ta shigo tare da binta da kll tace "um! Uwar ado da kwalliya kenan to kinyi a dai-'dai kije yaya Abbas na jiranki."
yaya Abbas kuma?? Zahra tayi saurin tmby tare da cewa "naje ya tozartani kome??"
safiyya ta tako tare da ca"tayaya zai tozartaki??"
to tayaya.???kafin muwuce seMUYI NAZARI
Aßdool-azeez ßeen Aßoußakar kena muku barka da darenku dakuma xapi..
Ko ince ruwa...
Title :
Zafin So Part 5
Description : *Ita kuwa maryama bin motarsa kawai tayi da kll har sai data daina hangota. Wani murmushine ke tashi daga fuskarta ta dawo da kllnta ga...
Rating :
5