Sai da suka shafe tsawon lokaci a haka sannan a hnkl kafarta ta fara takawa izuwa inda yake idonta nakansa, sai data matso gaf dashi sannan ta furta sunansa.
ABBAS!!
na'am MARYAMA!!
shima ya fada.
Lkc guda wani yalwataccen murmushi ya fadada a fuskarta, ranta yakai makurar dadi da ganinsa ba tare da tsammani ba.
Abnd ya fara zuwar mata a ranta shine sanda zasu rabu, a dai-dai nan ne yake sanar mata da tfyrsa, yake bata hkr gami dayi mata alkawarin dawowa.
A wancan lkcn hawaye ne a idonta, yau kuma gashi murmushi da farin ciki a tare da ita.
Ta kara rage tazarar dake tsakaninsu sannan tace "ashe zaka dawo??
Ashe baka manta dani ba??
Ashe mafarkin da nake zai tbbta!"
takai karshen maganar sanda ta karasa jikin motar.
Ya juyo tare da dubanta yayi murmushi yace "dama ai na gaya miki duk dadewa dole zan dawo gareki bazan taba mantawa dake ba, tayaya ma zan manta da rayuwata??"
ya fada sanda ya juyo suka dubi juna.
Yaushe ka dawo??
Tayi saurin tambayarsa.
Yace "yau na dawo, banso nayi iyakar kokarina na bari sai gobe da safe nazo amma na kasa jurewa, sbd zuciyata ta zaku tayi ido hudu da fuskar data shafe tsawon shekaru uku batayi tozali da ita ba."
Murmushi mai kama da kunya ya sake fadada a fuskar maryama a hnkl tace "na dade ina bawa zuciyata yakinin cewa zaka dawo sbd ina da tbbtcn kai ba mayaudari bane kuma bason wasa kake yimin ba.
Duk da cewa ina yawan tmbyr kaina me yasa na bari har nayi zurfi akan son wanda ba tsarata ba, wanda yafini komai a rywr duniya sai dai nakanyi saurin bawa kaina amsar cewa rabo ne dani shi yasa Allah ya nufeni da samun wanda nake so shima yana kaunata kuma kulawa a gareni."
Abbas yakai kllnsa ga sararin wurin da suke sannan ya dubeta yace "bana so ki rinka kawowa cewa akwai wani banbanci tsakaninmu, ni dake da kowa duka bayin Allah ne, fifikon dukiya da matsayi ba sune ababan takama ba sbd Allah ke bada su ba dabarar mutum ba.
Ki rinka dauka cewa kema kamar kowa kike ki saki jikinki ni Abbas nayi miki alkawarin ba abnd zai rabamu sai mutuwa." binsa tayi da kll kawai sbd ta tbbtr da gaske yake domin babu alamar wasa a ciki, zuwa can tace "akwai babbar magana kuma albishir amma muje wajen mama hajjo ta fada maka."
amma me yasa sai ita? Ke ba zaki fada min ba?? Abbas ya tambaya.
Ta wurga idonta tare da cewa "idan da hakki nane na fada maka da zanfi kowa farin ciki da hakan, amma ba'a bakina yakamata kaji ba daga bakinta ne sbd itace uwata kuma ubana."
Abbas ya gyada kai ya sake yin murmushi tare da cewa "to muje??"
gyada kai kawai tayi suka jera tare ckn hirar me cike da nishadi suka jera tare da nufar wani dan madaidaicin gini dake nesa kadan dasu.
zaune a kujera wata farar kamilalliyar mata ce dake sanye da fararen kaya idonta na sanye da farin glass, faffadan tebiri ne a gbnta wanda ke dauke da files da sauran takardu.
Wani mutum ne ke tsaye bayanda ya mika mata takardar dake hannunsa, ta dago kai tare da ce masa "ka tbbta dai abnd aka turo zai kai yadda zai wadaci yarannan ko??"
yayi saurin daga kai da cewa "wlh ranki ya dade zai isa don bana jin ma idan an taba kawo me yawan na wannan karon.
Ok! To kaje ka kula da yadda za'a shigar dasu store kafin ka dawo nasa musu hannu sai ka karbi takardar."
to ranki ya dade.
Ya fada tare da juyawa, dai-dai sanda ya fita ne Abbas da maryama ke shigowa gami da yin sallama.
Amsawa tayi da mamaki kuma tayi saurin daga glass din dake idonta.
Toh Abbas a gdn namu??
Allah ya nufi dawowa kenan??" Allah ya nufa na dawo.
Ya fada.
bismillah mana ku zauna.
Ta fada sanda tayi nuni da kujerun dake gabanta.
Sai da suka dan taba hira kadan sannan maryama tace "mama saiki fada masa."
sai da tadan bita da kll sannan ta juyo ga Abbas ta gyara zama tace "nasan zakayi mamaki idan na sanar maka cewa duk da tsawon shekaru 18 da maryama ta kwashe a wannan gida mun samu iyayenta na ainihi.."
da sauri ya dago kai cike da AL'AJABI, ya juya suka dubi juna shi da maryama sannan ya juyo yace "an samu iyayenta??
Bai jira amsa ba ya saki murmushi koba komai kalubalen da yake zaton fuskanta a auren maryama zai ragu ma2ka.
Taci gaba da cewa "sai dai sbd kai taki binsu, tace bazata je ba har sai ka dawo an fada maka kuma kasan inda ta tafi din gudun kada a samu akasi ta rasaka kasan tana sonka da yawa."
takai karshen maganar da sigar zolaya, maryama rufe fuskarta tayi cike da kunyarta.
Sun dauki lkc suna tattaunawa akan abin ba yawa sannan suka mike su, abbas ya zaro wani rubutaccen chak a aljihunsa tare da dorawa akan tebirin da fadin mama ga wannan ba yawa ko gero a siya a yiwa yara koko, tabi chak din da kll tare da fadin "ka dawo hidima ta dawo ko? Idan da irinku marayu ba zasuyi kuka ba Allah ya saka da alheri."
ameen suka fada a tare Abbas ya juya yayinda maryama ta matsa daf da ita ckn nuni da hannu tace "mama yanzu zan dawo."
maman ta daga kai kawai maryama ta juya tare da bin sahun abbas.
¤A hnkl kafafunsu ke takawa a tare ba tare da abbas ya dubeta ba yace "me yasa baki bi iyayenki kun tafi ba??"
tama tana me duban gabanta tace "sbd munyi alkawari dakai akan dawowarka ni kuma bana fata ace na saba alkawarin wanda ya yarda dani har ya bani ajiyar zuciyarsa."
amma wane tbbc gareki na cewa zan dawo??"
ya sake tambayarta.
Tun kafin ya rufe bakinsa tace "sbd na yarda dakai fiye da kowa a duniya."
cak suka tsaya sanda suka karaso jikin motar Abbas, yadan kura mata ido tare da cewa "a ina suke??"
ckn salo me kama da NAZARI tace "umm.. A garin hadejha ne can katsina, akwai full address din a rubuce a hnna."
Abbas ya kada kai tare da cewa "hkn yayi min dadi ma2ka ki bari ni zan kaiki da kaina."
nima zanso hkn, ace kaine mutum na farko da iyayena zasu gani a tare dani amma zamu iya tfy gobe??"
yayi dariya gami da dan harararta yace "sbd kinga na dawo shine har wani son ki tafi kike ko?? Zamu je amma ba gobe ba."
ta dago kai tare da cewa "sai jibi??"
ya grgz kai da fadin "a'a" ta sake tambayar "gata??"
ya kara grgz kai da fadin "a'a". Tayi dry tare da cewa "to sai yaushe??"
yace "kinga yau na dawo kuma dole akwai abubuwa da yawa da zanyi wadanda suka zama dole, ki bari sai nan da sati biyu sai muje."
idan kace sati 2 ranar litinin ta sama kenan??
Ta Fada.
Ya gyada kai da cewa "haka nake nufi."
tayi murmushi tare da cewa "Allah ya kaimu, nidai fatana da kuma farin cikina naganmu tare."
"nima haka" ya fada tare da ja da baya ya bude motarsa jim kadan ya fito ya tako gareta tare da mika mata abinda dake hannunsa da fadin "ga tsarabarki."
a hnkl ta karbi kwalin daya miko mata tabishi da kll tare da budewa kmr yadda ya fada, tabishi da kll kawai lkc guda ta zaro tamfatsetsiyar wayar sabuwa dal tana sheki da walkiya, tadan lumshe ido tare da cewa wannan fa??"
yace "wayace dana taho da ita musamman domin ke, don ke aka yita shi yasa zaki ga sunanki ne a jikin wayar kuma duk duniya ke kadai ce me irinta."
idonta nakan kyakykyawar wayar ta dago ta dubeshi tare da cewa "kayi abubuwa da yawa a rywt, kafi kowa kaunata a duniya bani da shakku akan haka..." ya katseta da cewa "a wajena har yanzu banyi miki komai ba sbd zan iya yin komai akanki", yadan kawo gwauron numfashi tare da cewa "bari na tafi ko? Sbd yamma tayi ki duba ckn wayar akwai lambata zaki iya kirana duk sanda so, sai mun hadu next time."
ta gyada kai kawai sai daya taka sannan tace "I always believed in you my everything."
yayi murmushi tare da cewa "i believe in you too."
ya karasa ga motar ya shiga tare da juyar da ita a hnkl ya sauke glass din suka dagawa juna hannu sannan ya taka motar ya wuce kai tsaye kuma gida ya nufa, abnd ya tbbtr a ransa shine lokacin boye-boye ya wuce yanzu lkc yayi da kowa zai san cewa MARYAMA ce zabinsa.
Title :
Zafin So Part 4
Description : Sai da suka shafe tsawon lokaci a haka sannan a hnkl kafarta ta fara takawa izuwa inda yake idonta nakansa, sai data matso gaf dashi sann...
Rating :
5