idonsa nakan hoton ya mike tsaye ya fara tattakawa kmr meyin safa da marwa nadan wani lokaci kuma ya saki murmushin karshe tare da dawowa gaban sif din tasa ya mayar da hoton inda yake ya rufe ya mike kai tsaye izuwa gadon ya kwanta.
Tunane- tunane yayi tayi har izuwa sanda barci ya kwasheshi kasancewar da gajiya a jikinsa sosai.
sai wajen la'asar ya tashi kai tsaye bathroom ya wuce yayi wanka ya dawo dakin nasa yayi sallah, bayan ya gama ne kuma ya wuce ma'ajiyar kayansa ya canja sabon dressing.
Kasancewarsa saurayi me cikar halitta yasa duk kayan da yasa ke ma2kar yi masa kyau musamman wannan da take ta musamman, kai kana ganin shigar da yayi kasan inda yake nufin zuwa babban guri ne a gareshi.
Da kwamemen koren takalmin dake kafarsa ya tako gaban tafkeken mudubin dake dakin nasa yabi shigar kananan kayan nasa da kallo sai a sannan ne ya dora faffadan bakin glass din dake hannunsa izuwa idonsa, ya shafi yalwataccen gashin kansa gami da sarawa kansa byn dashi kansa ya tbbtr shigar tayi masa kyau.
ya koma ga sif dinsa ya bude wata cover dake cike da mukullan mota yadau guda daya ya mayar ya rufe tare da juyawa yabar dakin.
zaune a falon su biyu ne kmr yadda suka saba, hira suke sosai motsin fitowarsa ne ya dawo da hankalinsu.
Safiyya tayi saurin sakin murmushi me kama da dariya tace "um! Dan gaye, iya daukar wanka da kansa ina zuwa haka??
Kmr bai jita ba yayi sai daya taKo izuwa gabansu sannan yace " Inda nake so zanje akwai wani abu ne??"
ta grgz kai tare da cewa "to kadai bi a hnkl kada ka bata kasan yanzu garin fa kmr yadda yake a baya bane, yanzu kaga akwai sabbin tituna, akwai sabbin gadar sama, kai har titin kasa anyi a garin nan."
zahra ta kwantar da kanta a kujerar da take kai tace "wanda ya dawo daga turai har a gaya masa ganin kyalkyale-kyalkyale??"
Abbas yayi saurin dago kansa yace "yauwa gaya mata dai y'ar gari, hmm.. Indai don wadannan ne to naku nanan wasan yara ne, na tabbata a titunan da akai muku duk dai irin nada ne, titunan kasar germany kuwa idan kika kalli kasa sai kinga fuskarki a ciki sbd kyalli da sheki, gadar sama kuwa kusan duk titi akwai ba kuma irin taku ba, na tbbt kuwa baki taba ganin inda aka fasa dutse daya kusa girman garinnan akai titi ta tsakiyarsa ba! To akwai a inda na baro."
safiyya ta kada kai tare da cewa "amma ai da haka muma wataran zamu kai duk inda suka kai, amma dai serious nake gaya ka kula."
Abbas ya gyada kai yace "bama wani nisa zanyi ba wajen IMRAN zanje..." kace wurin aminin naka zaka je??
Safiyya tayi saurin katseshi.
Ya gyada kai da cewa "Eh! Daga can kuma zanje wani wuri duk dai ina nan ckn yankin nasarawa kinga ko ihu na kwala zaku jiyo ni!!" duk sukai dariya.
Sai na dawo.
Ya fada sanda ya taka ya wuce.
"A dawo lfy!!" Dukkansu suka amsa.
Zahra tabishi da irin klln data saba yi masa sau daya suka hada ido ya dauke kansa yayi waje, tabi kofar fitar da kll ko kiftawa batayi.
Hakan yasa bama taji maganar da safiyya keyi ba har sai data taba ta, firgigit kuma tayi.
Safiyya tabita da kll tare da cewa "har kin tafi tunani adan kankanin lkc lfy kuwa??" ba komai.
Zahra ta amsa tare da mayar da kanta ga makekiyar T.V dake manne a jikin bango.
¤Zurfin cikin zahra yakai kokoluwar kaiwa, ta shafe tsawon shekaru 17 a gdn sakamakon mahaifanta da suka rasu tun tana karamar yarinya, hakan yasa ta dawo gdnsu abbas din kasancewarta y'ar kanin mahaifinsu.
Duk duniya zahra take so da kauna face Abbas amma dai-dai da rana daya bata taba iya furta masa hakan ba, abnd kawai take kudircewa a ranta shine akwai lkc amma yaushe ne?? Amsar da ita kanta bata sani ba kenan.¤
Abbas yana fitowa harabar gdn kai tsaye motar daya dauko mukullinta ya dosa (Renault cv.7) wacce kusan kowa da ita yasanshi, yadda ya barta haka take har yanzu. Kai tsaye ya juyar da ita yayi waje tare da bin kwaltar da tayi kudu ya bullo ta kofar nasarawa ta da daukar kwaltar da tayi yamma.
Tafiya kadan yayi yaci birki a bakin wani madaidaicin gida, ya fito kai tsaye ya dufafi cikin gdn bai dakata ba har sai da ya isa falon tsakiyar falon gdn, wanda ke tsaye a tsakiyar falon suna hada ido ya saki shewa ya dunkule hannayensa biyu yayinda abbas dinma yayi hakan hannayen nasu suka hadu.
Ai yanzu nake shirin na taho gdn.. Abbas ya katseshi da cewa "ai gani ni nazo, sbd rashin mu2nci ma ko irin kiran nan a waya kaji na sauka lfy bakai ba."
imran yace "kaga daddy ne ya hadani da aiki wlh kasan yau ko ofis baizo ba sbd shirya tararka, duk yau sai yanzu na sami nutsuwa."
yaja hannunsa da cewa " Abbas ya kauda kai da cewa "badai ka zabi zama dan kasuwa ba?? Ai ka rinka wahala kenan."
imran yayi dariya yace " ba wata wahala yanayin aiki ne.. shikenan kaifa ka zama barrister ko??"
Abbas ya gyada kai tare sa cewa "na zama lauya kmr yadda na dade ina buri, burina ya cika saura kuma buri daya rage min a duniya." da sauri imran yace "wanne buri kenan??"
Abbas ya taka tare da cewa "na auren MARYAMA".
Imran ya kauda kai da alama baiji dadin maganar ba zuwa can yace "wannan ta gdn marayun??"
abbas ya gyada kai tare da cewa "kwarai ina da wata maryama ne byn ita??"
imran ya numfasa yace "wlh a zatona tuni ka manta sa wannan yarinyar, sbd bazan daina gaya maka cewa baku dace da ita ba.
Gatanka da nata ba daya bane, kai! Kowa ya kalleta yaganka yasan kayi mata nisa, kamata yayi ace tsakaninka da ita sai dai ku gaisa idan kakai ziyara gdn marayu don agaza musu amma bawai aure ba."
Abbas ya dubeshi sosai yace "idan da wadannan kalaman naka zasuyi tasiri da tuni na rabu da ita, amma wlh duk sanda akai magana irin wannan son MARYAMA ne kawai ke karuwa a zcyta, yanzu ma haka can zanyi sbd idan ban ganta ba hnklna bazai taba kwanciya ba."
imran yace "shi yasa ko zama ka kasa yi??"
ai bazan zauna ba.. Ya juya tare da cewa "can zan tafi sai na dawo."
imran yabishi da kll yace "gdn marayun??" Abbas ya dakata ya juyo da cewa "eh gdn marayu kuma gdnsu maryama ba! Ko zaka rakani ne??"
imran yabishi da kll kawai sannan yace "A'AH nikam ina da abinyi, sai ka dawo."
Abbas ya juya kawai ya fice kai tsaye motarsa yahau yabar yankin gaba daya, inda yake burin zuwa.
Bai tsaya ba sai a bakin tafkeken gidan da ba'a hango karshensa sbd girmansa, ta bakin katuwar kofar shigar ya wuce da motarsa.
A hnkl yake tuka motar tunda ya shigo ckn gdn, duk inda ka kalla yara ne kanana da da matasa daban-daban suna harkokinsu.
Gine-gine ne daban-daban na makarantu, guraren kwana da sauransu.
*wasu ababan tausayin sai a irin wadannan guraren, yara ne abin tausayi iya ganinka wadanda nan ne kawai gatansu.
Sai daya je dai-dai inda yake son tsayawa sannan ya tsaya ya fito daga motar tare da jingina a jikinta, koda yake ta baya ya hangeta amma ya tbbtr itace.
*tsugunne take rike da hannun wasu yara biyu da alama akwai abinda take fada musu, lah! Aunty maryam ga uncle abbas can yazo.
Yarinyar ta fada.
Idanunta suka fara zarowa waje sbd mamaki, Abbas?? Ta fada.
A hnkl ta juyo da fuskarta daga inda take suka hada ido da sauri kuma ta saki hannun yaran tare da mikewa tsaye wani irin kll sukewa juna dako kiftawa basa yi.
ALLAH sarki love..
Nima daai allah kasa wacce nakeso tagane ina sonta...
Aßdool-azeez ßeen Aßoußakar
kena muku barka da dare..
Ilalliqa-a insha Allah...
Kasance da mu akodayaushe dan JOining din mu ko kuma
https://mobile.facebook.com/groups/461721127364011?view=group&refid=18