Wth---Aßdool-azeez ßeen Aßoußakar
Cikin mamaki taci gaba da kallon fuskar tashi, 2n safe take hakilo akansa don ganin tayi masa abnd zai faranta masa rai amma daga dawowarsa zai yi mata haka??
Ta dubeshi tace "yaya lfy kake hararata haka??
Kodai dama da haushi na ka dawo??
Da grgz kai yace "ba wani haushinki dana dawo dashi sai bayan na sauka a gdn nan ne dai kika bata min rai."
me kuma tayi??
Mominsu ta tambaya ckn alamun rashin fahimta.
Abbas ya gyara tsayuwa tare da cewa "nasan ita ta shirya girki a gdn nan shi yasa kamshi ya bade ko'ina har izuwa waje, mutanen dake waje suna jin kamshin amma ba lallai su ci abncn ba kinga an shiga hakkinsu."
safiyya ta kada kai tace "akan dai abinci ne ko??
Ta ai dama don kai nayi 2nda baka so bari na kwashe kayana..
Zahra zoki tayani mayar da abncn nan kitchen."
takai karshen maganar gami da takawa izuwa tebirin.
Da sauri ya dakatar da ita da cewa "ke bari mana! Zan dai taimaka miki inci ko kadan ne."
duk wanda ke falon sai da yayi dariya. Momin tace "daga dawowarka har kun fara ko? ..ai da ka barta ta kwashe abinta."
ina! Momi ai yanzu ba abnd nafi bukata kmr abnc da yunwa na dawo kinsan abncn turawannan ba wani rike ciki yake ba.
Abbas ya fada.
Safiyyar ta tako tare da cewa "kafin nan kawo jakar taka ko??
Ya mika mata da murmushinsa. Ta karba ya taka da sauri izuwa ga kujera ya zauna sannan suka shiga yin cikakkiyar gaisuwa irin ta wadanda suka dade basu hadu ba.
Abbas din ciki ya wuce sai kmr byn mintuna 30 ya dawo izuwa falon bayanda ya canja hatta suturar dake jikinsa, kai tsaye tebirin cin abncn ya wuce ya zauna ya dubi safiyya dake zaune a daya daga cikin kujerun dake zagaye da tebirin yace "a zuba min", ta dubeshi sannan ta dubi zahra tace "kinji wai a zuba masa to ai na siyarwa ne sai dai ka fadi kona nawa kake so.
Ya dubeta yace "idan na siyarwar ne ai kinsan zan iya siya kona nawa ne, amma dai ki aje wannan batun zuba min inci yunwa nake ji."
to kace 'don Allah' ta fada kmr me zare masa ido.
Ya gyada kai tare da cewa "to nace don Allah don annabi a zuba min."
zahra dake zaune ta kyalkyale da dariya tare da cewa "idan mutum yana kusa daku sai cikinsa yayi ciwo don dariya." ta kauda kanta kawai tare da cgb da abnd ya zaunar da ita a wurin, sai dai a ynz ba wani aiki da takeyi sai satar kallon kyakykyawar fuskar Abbas duk sanda ta lura idonsa ba'a kanta yake ba.
Har shi da kansa sai daya lura da hakan shima ya fara kallonta don yana son ya fahimci irin klln da take masa, ganin hakan zuwa can ta mike tare da cewa "safiyya idan kun gama hirar taku ina daki don na lura hirar bame karewa bace." toke kije daki kiyi me??
Safiyar tayi saurin tambayarta.
Abbas yace "kika sani ko nine ta gaji da gani a wurin??"
tayi saurin grgz kai tace "ah! Yaya nina isa? Aikin nan da mukayi ne kawai yasa na gaji."
to sai nazo. Safiyya ta fada.
Zahra tabi abbas da wani irin kallo wanda har sai daya sashi tsarguwa ta juya ta nufi dakinsu, tana shiga ta mayar da kofar ta rufe tare da jingina a jikinta ta saki murmushi zuwa can kuma ta taka izuwa cikin dakin ta zauna dai-dai sanda ta iso bakin tafkeken gadon dake dakin ta dakko faffadar wayarta tare da kamo wani kyakykyawan hoton Abbas dake cikin wayar ta kura masa ido.
Lkc guda tace "Allah sarki abbas dina nafi kowa farin ciki da dawowarka, zcyt tabar maraici daga yau kuma lkc yayi da zan furta maka kalmar dana dade ina boyewa I love you Abbas! Ta lumshe idonta gami da bin gadon ta kwanta.
¤a bangarensu abba
s kuwa sanda ta tashi abbas din har sai daya tafi dan gajeren tunani zuwa can ya dago kai tare da cewa "sister! Nifa ban gane klln nan da zahra keyi min ba, sai kace bata sanni ba??
Wai anya lfy take kuwa??"
dariya safiyyar tayi tare da cewa "lfyr ce ta kawo haka ai, ka sani ko sonka take yi??"
yayi saurin dakatawa da cokalin dake gaf da shiga bakinsa yace "SO kuma??" Safiyya tace "meye kuma na wani razana? Koka manta akwai aure tsakaninka da ita ne??
Kuma ai daddy zaiyi farin ciki da haka tunda y'ar kaninsa ce kaga sai ayi dakan daka shikar daka.."
kmr me harararta haka ya zaro mata ido ya ajiye cokalin dake hannunsa yace "kinga idan ma shawara kukayi da ita akan haka toki koma ki gaya mata zata wahalar da kanta ne kawai, kai! Wai sona tab! Aiki ja."
yakai karshen maganar da karfafa zancen nasa.
To me yasa??
Safiyya tayi saurin tambaya.
Abbas yabita da kll yace "meye naki na tambayata dalili wai kodai campaign kikeyi mata ne??
To idan ma wai gaya miki tayi ki fada min to ki koma ki fada mata cewa ta makara."
safiyya tayi dry tare da cewa "ni bamuyi haka da ita ba idan ma tana sonka ai tana da baki ko? Kuma ai mace ce son kowa kin wanda ya rasa idan kace baka sonta Allah zai bata wani.."
yauwa gara da kika ce wani amma bani ba.
Abbas yayi saurin fada.
Ta kauda kai tare da cewa "toyi hkr cgb da cin abncnka."
ya mike tsaye tare da cewa "ba za'a ci ba ki cinye kayanki."
ta gyada kai tare da cewa "dole kace haka mana 2nda ka koshi."
ko waigowa bai karayi ba ya wuce izuwa dakinsa, zama ya danyi na kmr mintuna biyar kwatsam ya tuno da ita, hoton fuskarta ya fara zaga idanunsa, sai yanzu ta fado masa a rai tabbas tana daya daga cikin na farko da zasu fara sanin dawowarsa.
Ya mike tsaye tare da da nufar y'ar madaidaiciyar sif dinsa ya bude wata cover ya zaro wani tafkeken hoto me ma2kar kyau ya kura masa ido, hoton wata kyakykyawar budurwa ce data wuce a misaltata musamman da yake an daukeshi sanda take murmushi, daga kasan hoton an rubuta suna MARYAMA. Murmushi ya fara tashi a fuskarsa, yasa hannu ya goge kurar da hoton yayi kyansa ya kara fitowa sosai. A hnkl kuma ya fara cewa "Allah sarki maryama na tsawon shekaru uku nayi rashinki yau na dawo kiris ya rage nazo har inda kike kmr yadda nayi miki alkawari a baya."
yaci gaba da bin hoton da kallo cike da murmushi dake nuni da tsananin son da yake yiwa wacce ke cikin hoton.
Eyyyah...amma Abbas baxakai gan ganciba kuwa????
To zadai muji...
Kasance da mu akodayaushe dan JOining din mu ko kuma
https://mobile.facebook.com/groups/461721127364011?view=group&refid=18