Goru dai wani kauye ne wanda jama'a ba su san da shi ba, amma sakamakon wannan lamarin gaba daya Nijeriya ta san da shi, bayan Idris Isma'ila ya yi wa 'ya'yansa guda ukku (Shamsudden, Fatahu da kuma Sharifat), yankan rago a lokacin da suke bacci. Bayan mahaifiyarsu ta barsu a kwance ta kewaye.
A lokacin da majiyarmu ta Daily Trust ta tattauna da matar Idris wacce take a cikin wani hali na rashin jin dadi, ta bayyana cewa, "Bayan na fita domin in kewaya, a lokacin yaran na kwance da mahaifin nasu suna bacci, dawowa ta ke da wuya sai na tarar da yaran kwance cikin jini, mahaifin nasu ya yanka su. Nan take na kwala ihu. Sai na fadi ina ta mirgina a kasa ina kuka nan take mutane suka zo domin su ba ni agaji. Dukkansu sai hankalinsu ya tashi a lokacin da suka ga abinda mijin nawa ya aikatawa 'ya'yansa".
Nafisa dai ta shaida cewa, mijin nata shi ya kashe 'ya'yan nasu ya tsare.
"Bayan auren mu mun dau lokaci mai tsawo ba mu taba samun sabani ba, amma faruwar wannan abu na samu rudani mai yawa, duk da yake a wasu lokuta yakan yi wasu abubuwa kamar mai tabin hankali. Amma hakan bai taba damar da ni ba, kuma ban taba sanar da mahaifana ba, domin bai taba cutar dani ba" inji Nafisa.
Nafisa ta kara da cewa, aduk lokacin da wannan halin nasa (na tabin hankali) ya tashi yakan sha wani magani domin ya dawo a hayyacinsa.
Yahaya Isma'il babban yayan mijin na Nafisa Ya shaidawa Dailytrust cewa, bayan kanen nasa Idris Sama'ila ya aikata wannan mummunan aiki sai ya tsere, ya fada cikin wata rijiya dake tsakiyar garin na Goru.
"Wasu mutane da suka ganshi a lokacin da yake wannan gudu su suka shaida mana haka sai muka kira 'yan sanda muka je tare da su. Muka fitar da shi daga rijiyar yana a raye bayan haka sai 'yan sanda suka wuce da shi". Inji Yahaya Isma'il.
Ya ci gaba da Cewa, "Da farko sun ajiye shi a garin Yeldu daga baya kuma suka tafi da shi Kangiwa, amma a yanzu haka yana asibitin tababbu wacce take a garin Jega".
Dan uwan na sa ya shaida cewa, ba a taba samunsa a cikin wani tashin hankali ba. Hasalima mafi akasarin lokuta yakan zauna a wani lungu yana ihu amma dai bai taba cutar da kowa ba kuma bai taba cutar da matarsa ba. Kuma a kowane lokaci tare da matarsa suke kwana a bukkarsu.
Ya kara da cewa da a ce suna samun sabani da matarsa da ba za ta kasance a tare da shi ba a tsawon shekarun da suka yi a tare ba.
'Yan kauyen sun shaida cewa, yanzu haka hukuma da gwamnati na ci gaba da bincike akan lamarin, kuma har gwamna ya ziyarci kauyen.
Makusantan Idris dai sun shaida cewa, Idris Isma'ila a duk lokacin damina yakan yi noma tare da tara itace domin ya sayar ya ciyar da iyalinsa.
Mahaifin Idris, Malam Adamu Muhammad ya shaidawa Dailytrust cewa, Dan nasa ya yi fama da lalurar tabin hankali tsawon shekaru uku da suka gabata. Bayan ya dawo daga gona. Tun daga wannan lokacin dabi'unsa suka canja kuma mun kai shi wurare da dama domin yin magani. Kuma a duk lokacin da rashin lafiyarsa ta motsa akwai maganin da muke ba shi domin ya dawo a hayyacinsa.
Title :
Yanda Mijina Ya Kashe Min Ya'yana Guda Uku
Description : Goru dai wani kauye ne wanda jama'a ba su san da shi ba, amma sakamakon wannan lamarin gaba daya Nijeriya ta san da shi, bayan Idris Ism...
Rating :
5