Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta bayyana a yammacin yau Talata cewa, an ceto Misis Iyabo Anisulowo a wani kauye da ake kira Gbegbelawo dake garin Olorunda a karamar hukumar Yewa ta Arewa a jihar Ogun.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan, Muyiwa Adejobi ya bayyanawa majiyarmu ta Premium Times cewa matar mai shekaru 65 an ceto ta ne da misalin karfe bakwai na yammacin yau. Ya kuma kara da cewa an kama wadanda ake zargin sun yi garkuwa da ita.
Title :
Yan Sanda Sun Ceto Tsohuwar Ministar Da Aka Yi Garkuwa Da Ita
Description : Rundunar 'yan sandan jihar Ogun ta bayyana a yammacin yau Talata cewa, an ceto Misis Iyabo Anisulowo a wani kauye da ake kira Gbegbelaw...
Rating :
5