Daga Alkasim Muhammad
Hausawa suna cewa da rashin kira karen bebe ya bata? Ni fa na fi son komai a jarraba, in an ci riba madalla, in kuma kasuwa ta yi kwantai sai a yi qoqarin gano masabbabi don kauce wa gaba, amma sam ban yarda da cewa an san haka za ta kaya shi kenan a haqura ba.
.
Koda kuwa a wajen neman aure ne, a ganina ba abin kunya ba ne ka nemi wata mace kan ta ba ka hadin kai don ka yi wa mahaifanta magana ita kuwa ta ce ta qi.
.
Wannan a wurina ya fi sauqi sau 100 da a ce ta nuna ba ta yi da kai, kai kuma ka na ce kan cewa sai ka aure ta, har ka nace sai ka kai ta rayuwar da za a fara bayan aure, macen da ce maka ba ta son ka ta sauqaqa maka, don ko ta aure ka ba dadinta za ka ji ba.
.
Au, to in dai ba tsafaceni kika yi ba ai komai ya zo da sauqi, na tabbata cewa duk lokacin da kika ce ba kya qaunata, wata jira kawai take yi na furta, shi kenan sai na fara neman inda take.
.
To ba ga mace kadai ba hatta namijin ma a wurin mace duk daya ne, in wani ya kwanta miki a rai kuma kin amince da addininsa da dabi'unsa, kina da damar da za ki mai da shi naki, ki jarraba kawai.
.
Akwai hanyoyi daban-daban na nuna manufa, wasu lokutan ma namiji bai sanin akwai hanya sai an nuna masa, shi kenan sai a gwada kawai, abin da Allah SW ya tsana shi ne a saba wa shari'a.
.
Ba laifi wata qawarki da kika amince da ita ta isar da saqonki a kaikaice, ita ta san lokacin da ya dace da irin saqon da za ta isar, sau da yawa in aka yi sara a kan gaba nan take ake karya abin da ake buqata.
.
Don mace ta yi gaban kanta ta ce wa namiji "Ina son aurenka" ba yau aka fara ba, mun karanta a tarihi cewa ya auku a zamanin Annabi, haka kuma mace ta tura wata aminyarta zuwa ga wani namiji shi ma ba baqo ba ne.
.
In buqata ta biya shi kenan, da ma abin da ake so kenan, in kuma an sami matsala a tsakiya, yadda wanda aka je wajensa bai da ra'ayi shi kenan, nan gaba wanda za a fuskanta sai ya dauki wani salo na masamman.