Daga Jarida Rariya
Tsagerun Niger Delta sun kai hare-hare kan bututun man fetur na kamfanin NNPC a yankin.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya rawaito wani mai magana daga yankin yana fadar haka a jiya Juma'a.
Ya kara da cewa an kai harin ne a daren Alhamis, akan bututun man, inji mai maganar kuma shi ne yake daukar man fetur zuwa matatar man na Warri da kuma wasu sassa da dama na kasar.
Eric omare dan kungiyar matasan kabilar Ijowo ya bayyana cewa an kai harin ne kauyen ogbe Ijoh kusa da wari.
Tsagerun Niger Delta sun sha kai hare hare kan bututun man na NNPC wanda yake jawo cikas a ayyukan tatar mai a cikin kasar.
Title :
Tsagerun Niger Delta Sun Kai Hari Kan Bututun Man Fetur Na NNPC A Yankin
Description : Daga Jarida Rariya Tsagerun Niger Delta sun kai hare-hare kan bututun man fetur na kamfanin NNPC a yankin. Kamfanin dillancin labaran Reu...
Rating :
5