Daga Rariya
Al'amarin wanda ya auku a garin Jibiya dake jihar Katsina, ya samo asali ne a lokacin da rashin fahimta akan bashi ya shiga tsakanin Amina da wata kawarta Hindatu. Har abun ya yi zafi ya kai ga Hindatu, ta gaya wa Amina mai maza biyu.
Wannan kalami a gaban mijin Amina, Hindatu ta furta shi. Wanda hakan ya girgiza mijin Amina kwarai. Inda nan take ya fassara, abun da cin mutunci da kuma batawa mai dakinsa suna. Bai yi wata-wata ba ya shigar da kara kotu.
Sanda kotu karanta wa Hindatu tuhumar da ake yi mata, Hindatu ta tabbatar ma da kotu cewar tabbas, mazajen Amina guda biyu ne.
Hindatu ta shaidawa kotu ita ganau ce, ba jiyau ba, a dukkan auren da Amina, ta yi guda biyun.
Hindatu tace wa kotu ta san dukka mazajen nata kuma ta san dukka dakunanta. Ta kuma kara da cewa duka auren guda biyu ta sheda su.
Alkalin kotu Alhaji Kabir Hamisu Bello, ya dage shari'ar zuwa ranar 9, ga watan May 2016.
Amina dai ta auri mijinta na farko ne a shekara ta 1994 a cikin garin Katsina yayin da ta auri na biyu a garin Jibia watanni biyar da suka gabata, ba tare da ta rabu da mijinta na farko ba.
Wannan al'amari dai ya haifar da jayayya tsakanin mazan guda biyu, inda kowa ke ganin cewa matarsa ce ta aure kamar yadda Sa'adu Sulaiman, jami'in hulda da jama'a na karamar hukumar Jibia ya shaida manema labarai
Title :
Ta Auri Maza Biyu A Lokaci Guda A Jihar Katsina
Description : Daga Rariya Al'amarin wanda ya auku a garin Jibiya dake jihar Katsina, ya samo asali ne a lokacin da rashin fahimta akan bashi ya shig...
Rating :
5