Rundunar Sojojin Nijeriya ta kame mutumin da ake zargi ya kashe Janar Mamman Shuwa daya daga cikin gwarzayen Sojin kasar da suka yi yakin basasa.
A watan Nuwamban 2012 ne wasu ‘Yan bindiga da ake zargin ‘Yan boko Haram ne suka afka gidan Janar Mamman Shuwa a Maiduguri, inda suka bude masa wuta dab da lokacin da ya ke shirin zuwa Sallar Juma’a.
Kakakin rundunar Sojojin Kanal Usman Kukasheka ya bayyana cewa za a gabatar da mutumin a gaban manema labarai a bataliya da uku a birnin Kano.
Title :
Sojoji Sun Kama Wanda Ya Kashe Janar Mamman Shuwa
Description : Rundunar Sojojin Nijeriya ta kame mutumin da ake zargi ya kashe Janar Mamman Shuwa daya daga cikin gwarzayen Sojin kasar da suka yi yakin b...
Rating :
5