Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majlisar dattawa Sanata Shehu Sani, ya kai dauki ga wani yaro dan kimanin shekaru uku da haihuwa, mai suna Ibrahim Salisu, wanda yake fuskantar barazanar makancewa sakamakon wata cuta da yake fama da ita a idonsa, ta hanyar biyan kudin maganin aikin, na tsabar kudi har naira dubu dari uku nan take, a babban asibitin kasa mai kula da lafiyar idanuwa dake Kaduna.
Da yake jawabi a yayin bada cak din kudin ga mahaifin yaron, Sanata Shehu Sani bisa ga wakilci mai ba shi shawara akan harkokin siyasa Suleman Ahmad, ya ce ceto idon yaron daga makancewa ya zama wajibi, ta la'akari da muhimanci idanu da kuma rashin karfi na iyayen yaron, da kuma bayanin babban Likita na Asibitin, wanda ya bayyana cewar, cutar dake damun idon yaron ta yi karfi har ta taba kokon kan yaron, wanda idan ba a dauki mataki cikin gaggawa ba, idon zai mutu kuma zai harbi dayan idon.
A wata ziyara da Sanata Shehu Sani ya kai babban asibitin kula da lafiyar idanun ne a kwanakin baya, ya ga wannan yaron cikin mawuyacin hali, kuma ya yi wa iyayen yaron alkawarin biyan kudin aiki, sannan a wannan rana ta Laraba ya cika wannan alkawari ta hanyar bada cak din kudi na naira dubu dari uku, ga iyayen yaron.
Lokacin da yake bayani cikin hawaye, bayan ya amshi cak din kudin daga hannun mai baiwa Sanatan shawara akan harkokin siyasa Malam Suleman Ahmad, mahaifin yaron mai suna Malam Umar Salisu ya godewa Sanata Shehu Sani akan daukin da ya kawo musu, na ceton idanuwan dansu daga makancewa, inda ya ce da ba don shigowar Sanatan cikin al'amarin ba, to da Allah kadai ya san halin da za su shiga, sannan ya yi addu'a Allah ya biyawa Sanata Shehu Sani bukatunsa na alheri.
Title :
Sanata Shehu Sani Ya Ceto Idanuwan Wani Yaro Daga Makancewa
Description : Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majlisar dattawa Sanata Shehu Sani, ya kai dauki ga wani yaro dan kimanin shekaru uku da ha...
Rating :
5