Daga Rariya
Fitaccen jarumin finafinan Hausa wato Ali Nuhu, ya ce ya yi matukar kaduwa lokacin da ya ga wannan labari na cin zarafin karamin yaron da ko hankali bai mallaka ba.
Ali Nuhu ya fadi wannan magana ne a lokacin da suke zantawa da wakilin Jaridar RARIYA a Kano, Bashir Abdullahi El-Bash.
"Na yi kuka da idona a ranar ban yi baccin kirki ba, saboda tausayin wannan yaron babu abin da ya fado min a rai lokacin da na ga wannan rashin imani, sai fim dina mai suna: "Basma" saboda kusan tafiyarsu daya da wannan labarin. inji Ali Nuhu:
"Zan yi amfani da wannan damar na yi kira ga gwamnatin tarayyar Nijeriya, da na jihohi da su bullo da hanyoyin yaki da wadannan munanan dabi'u marasa kangado.
"Ni mutum ne mai matukar son zama da yara kananan, ina kaunarsu, saboda addu'ar kananan yara mai saurin karbuwa ce ga Allah, dan haka dole ne na yi bakin-ciki, idan wata masifa ta fada masu.
"Idan da mu 'yan fim za mu samu dama a wajen gwamnati, ko kungiyoyin da ke da alhakin yaki da irin wannan matsala, to da na shaida, mu kuma za mu yi amfani da basirarmu, da lokacimmu domin yaki da wannan matsalar ta cin zarafin kananan yara, saboda finafinan Hausa, na saurin isar da sako ga al'umma.
A karshe ina kira ga gwamnati da ta hukunta duk wanda ta samu da irin wannan rashin imani dai-dai da abin da ya aikata, kamar yanda doka ta yi tanadi".
Title :
Sai Da Na Zubar Da Hawaye Kan Labarin Yaron Da Kishoyoyin Mahaifiyarsa Suka Illata - Ali Nuhu
Description : Daga Rariya Fitaccen jarumin finafinan Hausa wato Ali Nuhu, ya ce ya yi matukar kaduwa lokacin da ya ga wannan labari na cin zarafin kar...
Rating :
5