A wane gagarumin farmaki da rundunar sojin Nijeriya suka kai wani daji da ba a bayyana ba a jihar Zamfara rundunar sojin ta samu nasarar tarwatsa gungun barayin tare da kakkabe sansanoninsu baki daya a dajin.
Da yake bayyanawa manema labaru, kakakin rundunar sojin Nijeriya Kanal Sani Usman Kukasheka, ya bayyana Bataliyar sojin Nijeriya ta samu nasarar tarwatsa wadanda ake zargin barayin shanu ne, a dajin, inda ya yi amannar sun gudu da raunukan harbin bindiga a jikinsu.
Kukasheka ya bayyana sun samu nasarar kwace manya manyan mukamai da albarusai masu dimbin yawa a sa sanin na barayin shanun. Haka kuma ya bayyana cewa a yunkurin da rundunar sojin take na karkakabe 'yan ta'adda dake dazukan jihohin Zamfara, Kebbi, Sokoto, Kaduna da Katsina, yanxu haka rundunar sojoji wadda aka yi wa lakabin Operation Sharan Daji sun samu galaba sosai akan 'yan ta'addar wadanda ya bayyana suna gab da kawo karshensu.
Title :
Rundunar Sojojin Nijeriya Ta Ruguza Sannanin Barayin Shanu A Jihar Zamfara
Description : A wane gagarumin farmaki da rundunar sojin Nijeriya suka kai wani daji da ba a bayyana ba a jihar Zamfara rundunar sojin ta samu nasarar ta...
Rating :
5