Daga Bashir Abdullahi El-Bash
Kasar Rasha ta ce ba za ta nemi Syria ba ta daina kai hare-haren ta akan Aleppo ba, kamar yadda karamin ministan harkokin wajen kasar Guennadi Gatilov ya sanar.
Mr. Gatilov, ya ce ba za su bukaci hakan ba saboda a cewar sa ya kamata a gane cewa mahukuntan na Damascos na yaki da ta'adanci ne.
Mahukuntan Amurka ne dai suka bukaci kasar Rasha da ta matsa lamba ga gwamnatin Syria domin ta daina kai hare-haren ta akan Aleppo.
Amurka ta bakin sakataren harkokin wajen ta Jonhn Kerry ta bukaci da a maido da yarjejeniyar tsagaita wuta a duk fadin kasar ta Syria musamman a Aleppo.
Rariya
Title :
Rasha Ba Za Ta Nemi Syria Ta Daina Kai Hare-Hare A Aleppo Ba
Description : Daga Bashir Abdullahi El-Bash Kasar Rasha ta ce ba za ta nemi Syria ba ta daina kai hare-haren ta akan Aleppo ba, kamar yadda karamin mini...
Rating :
5