Mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya sauka a garin Legas inda ya sauka ya kaddamar da wasu aiyuka a madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Anyi tsammanin zuwan shugaban kasan a yau Litinin 23 da kuma gobe Talata 24 ga watan Mayu domin ya kaddamar da wasu aikyuka a jihar.
A jiya ne malam Garba Shehu, jami’i mai hudda da jama’a na shugaban kasa buhari ya tabbatar da cewa shugaban kasar baya samu zuwa Legas din ba, amma bai bayar da dalilan rashin zuwan nashi ba.
Garin Legas ya cika da muna inda yayi niyyar daukar bakuncin shugaban kasar Najeriya. Sashen shugaban kasa na filin jirgin sama ma ya samu sabon yanayi duka a cikin shirin karbar shugaban kasar. Kimanin shekaru 14 ke nan tunda wani shugaban kasa ya ziyarci jihar.
Daga cikin abubuwan da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kaddamar sun hada da Lagos State Emergency Management Agency Rescue Unit (LASEMA) dake a Cappa, sabuwar hanya a Okoto dake a Isolo da kuma wasu kayan tsaro domin tabbatar da tsaro a cikin jihar.
Idan za’a iya tunawa, gwamnatin Jihar legas ta rushe kasuwar Oshoi wadda take a karkashin gada a cigaba da gyaran jihar da gwamnatin take aiwatarwa. Sannan kuma gwamnatin jihar ta rushe kuma ta kori yan kasuwar Mile 12 dake a jihar bayan da aka samu wata hayaniya tsakanin Hausawan dake wurin da kuma Yarrabawan wurin. Wannan ne ya sanya da yawa daga ciki Hausawa yan kasuwan wurin suka tashi daga nan suka koma jihar Ogun.
A ziyara da Gwamna Ganduje na kano ya kai ma takwaran sa na Legas, Gwamnan ya roki Gwmnatin Jihar Legas da kada ta kori yan kasuwan kma ta samar wasu da wurin zama.
A wani labarin kuma, tsohon gwamna Jihar Legas Asiwaju Bola Ahmad Tinuba ya gana da yan kungiyar kwadago domin ganin cewa sun janye yajin aikin da suka shiga. Tsohon gwamnan ya roke jama’ar Najeriya da su kara hakuri inda ya bayyana cewa zaya iya rantsewa cewa shugaban kasa Buhari ba zaya saci kudin Najeriya ba.
Title :
Photos: Osinbajo Ya Ziyarci Jihar Legas
Description : Mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya sauka a garin Legas inda ya sauka ya kaddamar da wasu aiyuka a madadin shugaban kasa Muha...
Rating :
5