Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya karyata zargin da al’ummar Kano ke yi masa na cewa ba'a ba kowane irin mutum mukami ko kwangila, har sai ya bi ta hannun mai dakinsa, inda ya ce wannan batu karya ne, yarfe ne irin na siyasa, wanda ba shi da tushe balle makama.
Ya kara da cewa a matsayinsa na Gwamna, mai dakinsa ba ta da wani tasirin da za'a ce sai an bi ta hannunta sannan zai ba wani mutum kwangila ko mukami, shi yana bayar da mukamansa da kwangila ne ga wanda ya cancanta.
Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da gamayyar kungiyoyin ma’aikata da ke karkashin kungiyar ma’aikata ta NLC, karkashin Shugabancin Kwamared Kabiru Ado Magayakin Munjibir ta kai masa ziyara a dakin taro na Africa House da ke gidan gwamnatin jihar Kano.
Daga karshe Gwamna Ganduje ya bayyana cewa ba wani abu ba ne ya kawo tsaikon kammala hanyoyin da ake aiwatarwa a Kananan Hukumumin jihar Kano 44 da gwamnatin Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ta bayar, sai matsalar rashin wadataccen kudin da gwamnatocin kasar nan ke fama da shi.
Title :
Ni Ba Mijin-Ta-Ce Ba Ne - Ganduje
Description : Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya karyata zargin da al’ummar Kano ke yi masa na cewa ba'a ba kowane irin mutum mukami...
Rating :
5