Rahotanni na cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yanke shawarar nada tsohon Kocin Chelsea, Jose Mourinho a matsayin sabon Kocin United din.
An yi amanna cewa hukumar gudanarwar Manchester United din ce ta cimma yarjejeniya irin ta fahinta da Morinho, gabannin karawar da ta yi da Crystal Palace, inda manchester United din ta samu nasara da 2-1, wadda ta samu damar lashe kofin FA.
Ana dai sa ran nan da wasu'yan kwanaki kungiyar Manchester United din za ta yi sanarwa ta musamman a kan nadin da ta yi wa Morinho a matsayin sabon Kocinta.
A watan Disamba da ya wuce ne dai kungiyar Chelsea ta sallami Morinho, wanda yana daga cikin manajojin da suka ci nasara a aikinsu, saboda ya jagoranci kungiyoyi daban-daban har uku da suka ci kofi a Turai.
Kocin Manchester United na yanzu, Louis Van Gaal na shan suka sakamakon gazawarsa wajen sama wa kulab din gurbi a gasar Champions League mai zuwa.
Title :
Manchester United Na Shirin Nada Mourinho
Description : Rahotanni na cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yanke shawarar nada tsohon Kocin Chelsea, Jose Mourinho a matsayin sabon Koc...
Rating :
5