Daga Jarida Rariya
A yayin da ake ganin kura Ta lafa a rikicin siyasar Kaduna, sabon rikici ya kunno kai a tsakanin dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani da Gwamnan Jihar, Malam Nasir El Rufa'i a sakamakon karin kudin fetur da gwamnati Ta yi.
Tun da farko dai, jam'iyyar APC reshen Kaduna tayi barazanar korar Sanata Shehu Sani bisa adawarsa ga gwamnatin Buhari kan matakin Kara kudin fetur, lamarin da ya janyo dan majalisar ya zargi El Rufa'i da makarkashiyar korarsa daga jam'iyyar. Haka kuma Sanata Shehu ya jaddada mubaya'arsa ga Shugaba Muhammadu Buhari.
Title :
Karin Kudin Fetur Ya Tunzura Rikicin Shehu Sani Da El Rufa'i
Description : Daga Jarida Rariya A yayin da ake ganin kura Ta lafa a rikicin siyasar Kaduna, sabon rikici ya kunno kai a tsakanin dan majalisa mai wakilt...
Rating :
5