Rahotanni daga Najeriya sun ce kamfanin mai na Chevron ya rufe ayyukansa na hakar mai a yankin Niger-Delta da ke kudancin kasar.
Kamfanin ya dauki wannan mataki ne sakamakon hare-haren da ake zargin wasu 'yan bindiga na kungiyar nan da ake kira Niger Delta Avengers ke zafafa kai wa.
A ranar Laraba da daddare ne 'yan bindigar suka kai wani harin a yankin Escravos inda kamfanin ke gudanar da ayyukansa.
Dama dai 'yan kungiyar na Niger Delta Avengers sun yi gargadi da kamfanin Chevron ya bar yankin zuwa karshen watan nan na Mayu.
Sulaiman Ibrahim ya tambayi wakilinmu na Enugu, AbdusSalam Ibrahim Ahmed karin bayani kan lamarin:
Title :
Kamfani Chevron Ta Dakatar Da Aiyuka Ta A Najeriya
Description : Rahotanni daga Najeriya sun ce kamfanin mai na Chevron ya rufe ayyukansa na hakar mai a yankin Niger-Delta da ke kudancin kasar. Kamfanin y...
Rating :
5