Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta Kama Mabarata su 25. An kama su ne da laifin karya doka, dokar da ta hana yin barace-barace a Titunan Birnin Kano.
Babban jami'i mai kula da hana barace-barace na Hukumar Hisba dake Kano, Mallam Musa Sangaya shi ya bayyanawa manema labarai afkuwar wannan lamari a yau Laraba.
Ya ce mutanen su sun kama mutun 25 ne a guraren Na'ibawa, 'Yankaba da Bata, ya kara da cewa daga cikin mutune 25 din da aka kama akwai tsofaffi da kananan yara.
Title :
Hukumar Hisba ta Jihar Kano Ta Kama Mutane 25 Da Laifin Yin Barace-Barace Akan Titi
Description : Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta Kama Mabarata su 25. An kama su ne da laifin karya doka, dokar da ta hana yin barace-barace a Titunan Birnin...
Rating :
5