A ranar Talatar da ta gabata ne aka ceto Amina Ali daga dajin Sambisa, fiye da shekara biyu bayan ƙungiyar Boko Haram ta sace ta daga makarantar sakandaren Chibok.
Amina Ali dai ita ce ta farko da aka ceto, cikin mata 219 da Boko Haram din suka yi garkuwa da su.
Ga dai abubuwan da aka sani game da ita:
Daya daga cikin shugabannin al'ummar Chibok, Hosea Abana Tsambido, ya shaida wa BBC cewa shekarar yarinyar 19, kuma ta fito ne daga Mbalala, wanda ya kai nisan kilomita 10 daga garin na Chibok.
Wani dan jarida Samson Aboku, wanda shi ma ya fito daga Mbalala , ya ce mutanen garin sun kai akalla 30,000 kuma yawancinsu mabiya addinin Kirista ne, amma ita Amina Musulma ce.
Samson ya kara da cewa, Amina ta girma ne a wata 'yar bukka tare da mahaifiyarta.
Baban ta ya rasu, amma cikin 'ya'ya 13 da uwar ta haifa, su biyu kacal, watau da Amina da yayanta, suka rayu.
Aboku Gaji, wanda ke jagorantar wasu kato da goran da suka tsinto Amina ya bayyana wa BBC yadda haduwar ta da mahaifiyarta ta kasance.
Ya ce, "Lokacin da muka iso gidansu, mun tarar da kofa a rufe, sai na ce maman nata ta fito ga bakuwa, tana ganin ta sai ta soma kiran sunan ta cikin mamaki, Amina! Amina!!.
Daga bisani sai suka rungume juna, har kamar za su fadi kasa, sai da muka rike su.
Aminar kuma sai ta soma bai wa uwarta baki, tana cewa 'Don Allah mama ki yi hakuri, ki kwantar da hankalin ki, ban taba tsammanin zan sake ganin ki ba, ki share hawayen ki. Allah Ya bamu damar sake haduwa.'
Haka nan Amina ta ce wa mahaifiyarta."
Blamadu Lawan, shi ne mataimakin shugaban makarantar sakandaren Chibok, inda Amina take kafin a sace ta, ya kuma shaida wa BBC cewa, Amina daliba ce mai nutsuwa.
Lawan ya ga lokacin da aka wuce da ita cikin gari ranar Laraba, inda ya ce ya ga duk ta canza kamanni, ta rame.
A lokacin da ta ke hannun Boko Haram, Amina ta haifi 'yar ta mace, wacce ake iya gani a wani hoto da sojojin Najeriya suka dauka.
Daya daga cikin masu fafutukar nan na #BringBackOurGirls, Hadiza Bala Usman, ta shaida wa BBC cewa watan jaririyar hudu.
A wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar, ta ce an ceto Amina ne tare da wani mutumi mai suna Mohammed Hayatu, wanda ya ce shi ne mijinta, duk da cewa sojojin na zargin sa da zama dan kungiyar Boko Haram.
Title :
Haduwa Amina Ali Nkeki, 'Yar Chibok Din Da Aka Ceto Da Mahaifiyarta
Description : A ranar Talatar da ta gabata ne aka ceto Amina Ali daga dajin Sambisa, fiye da shekara biyu bayan ƙungiyar Boko Haram ta sace ta daga makar...
Rating :
5