Gwamnatin tarayyya Ta bayyana dalilan kin sakin Tsohon Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Sambo Dasuki inda ta nuna cewa tsare shi na da alaka da abin da ya shafi sha'anin tsaron kasa kasancewa yana da hannu wajen karkatar da kudaden sayo makamai.
Da yake gabatar da hujjoji a gaban katun kungiyar ECOWAS, lauyan gwamnati, T.D Tijjani ya ci gaba da cewa an gano wasu makamai masu yawa a gidan Dasuki sannan kuma bayanan sirri sun nuna cewa akwai yiwuwar ya boye wasu makaman a wani wuri na daban.
Title :
Gwamnati Ta Bayyana Dalilan Kin Sakin Dasuki
Description : Gwamnatin tarayyya Ta bayyana dalilan kin sakin Tsohon Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Sambo Dasuki inda ta nuna cewa tsare shi na ...
Rating :
5