A karon farko, hukumar EFCC ta samu wata bukata na neman tuhumar Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan bisa rawrar da ya taka wajen karkatar da kudaden makamai fiye da Dala bilyan 1.3.
Wata majiya daga hukumar ta nuna cewa, wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Enugu, Ikenna Ijezie ne ya gabatar da wannan bukata wanda kuma tuni hukumar ta gabatar da kyafin bukatar ga fadan shugaban kasa.
Idan ba a manta ba, RARIYA ta ruwaito cewa tsohon Shugaban na zaman mafaka na Wucin gadi a kasar Kwaddibuwa bisa fargabar matakin cafke shi amma kuma daga baya tsohon shugaban ya musanta wannan rahoto yana mai cewa zai dawo Nijeriya ya fuskanci kowane irin kalubale.
Title :
EFCC Za Ta Tahumi Goodluck Jonathan
Description : A karon farko, hukumar EFCC ta samu wata bukata na neman tuhumar Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan bisa rawrar da ya taka wajen karkat...
Rating :
5