Dan majalisar dokokin na tarayya mai wakiltar mazabar Kachia/Kagarko a majalisar kasa ta Abuja, ya sha da kyar daga hannun wasu matasa wadanda suka fusata, inda suka afka mishi jim kadan bayan kammala taron ganawa da jama'a da gwamna Nasiru El Rufa'i ya yi da jama'ar sashin kudancin Kaduna a garin Kachia.
Dan majalisar mai suna Adams Jagaba, wata majiya ta bayyana cewar, matasan yankin nasu sun dade suna kule da shi, sakamakon kaurace musu da yake yi, da rashin yin wani katabus a majalisa, sannan uwa uba da batun sauya sheka da ya yi daga jam'iyyar APC da yayi takara a ciki zuwa PDP.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewar, matasan sun yi wa dan majalisar kofar rago ne bayan kammala taron da gwamnan ya yi, sannan wasu majiya karfi daga cikin su, suka yi kukan kura suka yi ta gabza masa naushi, har sai da suka kai shi kasa.
Daga bisani 'yan sanda sun tarwatsa matasan, inda suka kwashi dan majalisar ranga-ranga zuwa wani asibiti da ke kusa.
har ya zuwa lokacin hada rahoton nan Adams Jagaba yana gadon asibiti yana ci gaba da amsar magani.
Title :
Dan Majalisar Tarayya Adams Jagaba Yasha Da Kyar A Hannun Matasan Mazabarsa A Jihar Kaduna
Description : Dan majalisar dokokin na tarayya mai wakiltar mazabar Kachia/Kagarko a majalisar kasa ta Abuja, ya sha da kyar daga hannun wasu matasa wadan...
Rating :
5