Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi II ya bukaci a samar da wata doka da za ta haramta aurar da 'yan matan da ba su kai shekaru 18 ba.
Sarkin ya yi wannan kira ne yayin wani taron karawa juna sani da majalisar malaman addinin musulunci na Arewacin kasar nan suka shirya wanda aka gudanar a jiya Talata a jihar Kano.
Sarki Sanusi Lamido Sanusi II ya kara da cewar yanzu an wuce lokacin da iyaye za su rinka aurar da 'ya'yan su tun ba su san kansu ba.
Sarkin ya kuma bukaci da a samar da dokar da za ta hukunta wadanda suke yi wa 'ya'yan su auren wuri.
Title :
Bana Goyon Bayan Auren Wuri - Sarkin Kano
Description : Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi II ya bukaci a samar da wata doka da za ta haramta aurar da 'yan matan da ba su kai shekaru 18 ba. Sar...
Rating :
5