Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba lallai bane a gayyato tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan domin ya amsa tambayoyi game da batun badakalar cin hanci da rashawa da aka tafka a gwamnatinsa, musamman ma na kudin sayen makamai, inda Buhari ya ce Jonathan ya janyowa kansa kima da martaba a idon duniya sakamakon halayyar da ya nuna bayan zaben 2015.
Shugaba Bubari, wanda ya ce ya yi matukar mamaki a lokacin da ya ji Jonathan ya kira shi yana taya shi murnar cin zabe tun ma kafin a bayyana sakamakon zabe, ya kara da cewa ba zai taba mancewa da irin wannan halayya ba a rayuwarsa.
Title :
Ba Zan Taba Mancewa Da Jonathan Ba - Buhari
Description : Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba lallai bane a gayyato tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan domin ya amsa tambayoyi game...
Rating :
5