A kokarin ta na zakukulo ragowan ‘ya’yan kungiyan Boko Haram da ke fakewa a kauyuka da birane, rudunan 22 na sojoji dake karkashin shirin LAFIYA DOLE, a jiya Lahadi ta share kauyuka hudu daga ragowan ‘yan ta’addan na Boko Haram. Rundunan sojin wanda ta fitar da sanarwa ta hannun daraktan yada labaran ta mai rikon kwarya kanal Sani Kukasheka, ta ce ‘yan ta’addan wadanda ke labe a yankunan Cinga, Mallum Maja, Bosuma da kuma kauyen Murye, an same su da muggan makamai inda suka kasance barazana ga al’ummar yankin.
‘Yayin arangama da su da jami’an na soji suka yi da su, ‘yan kungiyan na Boko Haram uku sun mutu yayin da aka kama mutum tara wadanda suka buya a cikin ramuka inda aka zakulo su kuma aka kame su da rai. An kuma same su da Bindigogi guda 9, adduna guda 3, kwari da baka da kuma baburan hawa guda shida wanda suke amfani da su wajen zirga zirga. Har ila yau, an gano babur guda daya, janareta da kuma na’urar samar da wuta dake amfani da hasken rana.Jami’an sojin suka ce sun kwato garken shanu wanda yawan shanaye ya kai 300 daga ‘yan Boko Haram din wanda suka sace daga makiyaya Fulani, wanda nan take aka mayar wa masu shi.Sanarwan ta tabbatar da cewa, rundunar sojojin ta tseratar da mutane 400 wanda ‘yan kungiyan na Boko Haram suka yi garkuwa da su.Sanarwan ta bayyana cewe babu wanda ya rasa ranshi yayin arangamar daga rundunan na sojoji kuma babu wanda ya samu rauni.
Rariya
Title :
An Ceto Mutane 400 Da Shanu Guda 300 Daga Wurin 'Yan Boko Haram
Description : A kokarin ta na zakukulo ragowan ‘ya’yan kungiyan Boko Haram da ke fakewa a kauyuka da birane, rudunan 22 na sojoji dake karkashin shirin L...
Rating :
5