Nagode Wa Allah Babu Wani Abin Zargi Da Aka Gano A Gidana, Inji Malam Shekarau
"Kamar yadda wani ya rubuta a cikin jawabinsa cewa an ba ni naira milyan 25 a lokacin aikin zaben 2015. Na yi tuhuma ga wanda ya bada wannan jawabi a gaban jami'an tsaro na mene ne hujjarsa? Ya ce ai tunda an ce za a baiwa shugabanni 25 kuma shi ma an ba shi, to yana kyautata zaton ni ma an ba ni, shi ya sa ya ambata cewa an ba ni.
"Ni kuma na ce ba milyan 25 ba, ko naira daya ce ba zan bayar ba sai an kawo min hujja karbabbiya. Wanda ya ba ni ya zo ya ce ga sanda ya ba ni, ga wurin da ya ba ni, ga lokacin da ya bayar.
"Idan ba a bada wannan hujja ba, a shirye nake da na zauna tare da su idan ma shekara nawa ne, sai an bijiro da hujjar nan, ko kuma mu je gaban alkali har sai an bijiro da hujjar.
"Kuma an zo an birkice ko ina a cikin gidana, Allah da ikonsa ba a samu wani abu kwaya daya ba wanda yake da dangantaka na zargi, na kowane irin abin da ya shafi kudi. Ina mai godiya ga Allah da wannan abu da ya taso ya zama alkairi, domin su da kan su sun gani.
"Na kuma ba su lambar asusu na domin a bi sahu a ga me ya shiga ya fita daga nan har zuwa shekara 20 da suka wuce. Ba ni da wani asusu da ya wuce wannan.
"Ina kira ga al'umma (masoyana) su kwantar da hankalinsu babu damuwa a ciki, al'amari idan ya zo daga Allah na kaddara, mai dadi da mara dadi a shirye muke da mu karbe shi.
"Manzon Allah (SAW) ya sanar da mu cewa tsayawa kan gaskiya ba ya hana a sha wuya, amma ba za a taba jin kunya ba. Don haka kowace irin tuhuma a shirye muke da mu fuskance ta, idan an zo mana da hujja. Ba mu ce mun fi kowa iyawa ba, ba mu ce mu ba za mu yi kuskure ba.
"Annabi (SAW) ya ce kowane dan Adam mai kuskure ne, don haka ranar da duk aka hangi inda muka yi kuskure a sanar da mu, kuma a shirye muke da a tuhume mu kuma mu bada amsa.
"Bana zargin kowa kuma bana zargin al'amari na siyasa, ni a wuri na Allah ne ya bijiro da jarrabawa don ya yi amfani da ita ya bayyana wani al'amari wanda watakila yake boye.
"Domin a cikin hikimarsa Allah ya kan yi amfani da hannun Shaidan ma ya tallata wani abu na alheri.
"Bana zargin kowa. Kuma bana zargin wani ko wata siyasa ko wata hamayya ta siyasa. Na kaddara Allah ne ya kawo sanadi. Amma tunda bincike yana nan ba gamawa aka yi ba, an bada beli an cika ka'idoji da aka saba bayarwa na kowace irin hukuma. Za a ci gaba da bincike, kuma za mu ci gaba da sauraren me za a bijiro da shi na bayan binciken.
"Muna rokon Allah ya tabbatar da gaskiyar al'amura Insha Allah.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya yi wannan jawabin ne yau a taron manema labarai da ya gayyata bayan hukumar ta EFCC ta bada belinsa.
Title :
A Shirye Nake Da Duk Wata Tuhuma Da Za A Yi Min - Shekarau
Description : Nagode Wa Allah Babu Wani Abin Zargi Da Aka Gano A Gidana, Inji Malam Shekarau "Kamar yadda wani ya rubuta a cikin jawabinsa cewa an b...
Rating :
5