Misalin karfe 12:00 na tsakar ranar wacce ke
tsakiyar daukar zafi hamshakin katafaren jirgin saman nan kuma sananne wato TURKISH airline ke
kokarin sauka izuwa doron kasa a makeken filin
jirgin kanon dabo (AMINU KANO INTERNATIONAL
AIRPORT).
Kasancewar tuni ansan da saukarsa yasa duk
ma'aikatan dake filin jirgin saman suka kasance cikin shiri, dukkan airport din yadau harama
saukar tasa kawai suke jira.
Sai daya tsaya cakk! A sama na wasu y'an
sakwanni sannan bayan tbbtr da dai-daituwar
komai ne kuma a hnkl ya fara yo kasa hakan yasa
gigitacciyar kararsa ke karuwa a hankali. Bada jimawa sosai ba ya dira a dandaryar kasa a
hankali kuma kafcecen jirgin ya fara tafiya bisa
dandaryar kasa har izuwa inda aka tanada don
tsayawarsa, cak kuma ya tsaya din.
Sai byn wasu y'an mintuna kadan ne mutanen
dake cikin jirgin suka fara fitowa tare da sakkowa ta matattakalar da aka tanada don sakkowa,
kasantuwar jirgin private wanda na manyan masu
ji da kansu ne ke cikinsa yasa ba wasu mutane ne
masu ma2kar yawa a cikinsa ba.
*kmr yadda yake a dokance nan da nan ma'aikata
na hukumomin dake kula da shige da fice daban- daban suka yo rufdugu don tabbatar da cewa ba
wanda ya shigo da wani mugun abu da aka saba
safararsa daga kasa zuwa kasa, jakunkuna, jiki
dama komai sai an bincika banda na'urori masu
gani har hanji dake tbbtr da tantancewa kafin
wucewar ko wanne daya daga cikin matafiyan. Cikin jerin mutanen da suka dira ba dadewa harda
wani saurayi wanda kll daya kawai zakayi masa ya
fita daban da sauran mutanen koda kwatance
za'ayi zaiyi saurin ganowa bare kuma idan laifi yayi
ba wuya za'a kamashi, fari ne sol da babu digon
baki a jikinsa ko kadan kai sai ka rantse baturene ziyara kawai ya kawo najeria.
yana da kyan zubi da yanayi gami da birgewa, kll
daya zakayi masa kasan ba wani abu dake
damunsa ko kadan.
A hnkl yake takawa da kafarsa me sanye da bakin
takalmin daya rufe kafarsa gaba daya, wando da rigar kuwa na suit ne a jikinsa ruwan toka (ash
colour).
Kansa ba hula sai dai bakin kyakykyawan
yalwataccen gashin kansa wanda ya matukar fito
da kyakykyawar halittarsa, rike yake da wata
madaidaiciyar jaka ta matafiya da yake jaye da ita. Kyam! Ya tsaya a gaban jami'an dake tbbtr da
kasantuwar ba wani gogaggen criminal daya
sauka da illegal products a airport din, jagoran
masu sa ido akan wadanda suka sauka ba
dadewar siririn mutumin dake ta zare ido kmr yaci
babu na tsaye yasawa na'urorin ido kadan yake jira ta bankado cewa ga wani da bindugu, bama-
bama, illegal drugs ko uwa uba cocaine tofa
wannan ya shiga dubu na bala'i.
"kai! kalli nan."
mutumin ya fadawa saurayin dake tsaye a
gabansa, bayan ya dubeshi dinne kuma yace "menene a jikinka??
Da kuma wannan jakar dake hannunka??"
cikin salo na tsoratarwa.
Ba wata fargaba saurayin ya daga kansa ya
dubeshi tare da wurga idonsa ga sauran jami'an da
duk fuskarsu ke a turbune yace "jikina ba komai, jakata ce gatanan kaya nane a...,
kai! Wai meye ma zan bata lokacina wajen gaya
maka bayan ai kana takama da na'ura me gani har
ciki ko??
Ka tambayeta mana ta gaya maka ko kuma kuzo
ku bincika idan itama din baka yarda da ita ba." mutumin ya bishi da kll tare da kada kai yace "kai
wannan bazaka wuce ba tukunna koma gefen can
ka tsaya."
mutumin ya fada yana zare ido kmr zaici babu.
Da kll me kama da harara saurayin yabishi tare da
cewa "akan wane dalili to?? An kamani da wani laifi ne??"
a'ah! Ai ba'a tbbtr da laifi ko rashinsa sai an
kammala bincike kai kuma ba'a gama bincikarka
ba shi yasa bance ka wuce ko kuma a kamaka ba
sai nace ka koma gefe.
Mutumin ya fada har yanzu fuskarsa a daure take. Kyakykyawan saurayin ya tabe baki gami da
kauda kai yaja jakarsa ya koma gefe ko kadan ba
wani damuwa ko tashin hnkl a fuskarsa duk da
zaratan jami'an tsaro iri-iri daketa kaiwa da
komowa a tafkeken kayataccen filin jirgin daya
daga cikin mafiya girma a najeriya. Akalla mintuna ashirin ya kwashe a tsaye yana
binsu da kallo kawai, da alama ba karamin yarda
da kansa yayi ba.
jakarsa kawai ya kafe ta zame masa kamar abin
dogarawa, binsu kawai yake da kallo daya bayan
daya yana dauke kai. Sai da ya zamana duk wadanda suka sauka tare
sun fice sai shi kadai ya rage sannan shugaban
masu binciken ya tako izuwa gabansa ya tsaya
suka dubi juna bisa mamaki a karon farko ya saki
fuska yace "Abbas dan Alhaji abdulmumin sada
ko?? Baka wani tsorata ko grgz ba kuma babu alamar
fargaba a tare dakai me yasa??"
saurayin yace "idan kaga fargaba da tsorata to
babu gsky ne ni kuma ina da ita mezai dameni??"
duk da wadannan ma'aikatan da kuma hatsarin da
wurinnan keda shi?? Mutumin ya tambaya.
Saurayin ya kada kai yace "hmm.. Karka manta
daga germany nake yanzu haka na tbbtr kuwa can
yafi nan tsaro, hatsari da kuma samatsi banda
zunzurutun kayan aiki wanda ko sauro ka boye sai
an gane." ya kauda kansa a zcyrsa yace "duk criminal din
daya tsallake tantancewar can yazo nan har kuka
iya kamashi ai shi yaso wlh."
mutumin yayi murmushi yace "mahaifinka na
kaunarka ma2ka, tun jiya yazo yake gaya mana
cewa yau zaka sauka kada mu barka ka tafi har sai yazo sbd ka dade rabonka da kasar nan kuma
yasan halinka akwai karanbani zaka iya cewa zaka
gane gida wanda ba lallai ba sbd garin abubuwa
da yawa sun canja...
Ga masu tarar taka can ma sun iso!"
yayi nuni da wata luxury data shigo yanzu, ya mikawa Abbas din hannu suka gaisa tare cewa"da
fatan ka fahimci dalilinmu na dakatar dakai, you are
wellcome back to nigeria."
ya fada tare da juyawa ya koma ga bakin aikinsa.
Abbas yabishi da kll tare da juyawa ya dubi
mahaifinsa da tuni ya fito motar da suka shigo ba dadewa, ya saki murmushi tare da jan jakarsa ya
nufi inda suke da saurinsa.
Tun kafin ya karaso mahaifin nasa fuskarsa a sake
yana me kada kai yace "you are wellcome my son
da fatan an iso lfy??"
cak ya tsaya a gabansa cike da murmushi yace " lfy kalau my dad."
da fatan ba wata matsala da kaci karo da ita a
germany??
Mahaifin nasa ya sake tambayarsa.
Ya gyada kai tare da cewa "ba wata matsala dad
komai ya tafi dai-dai, zanso mu wuce gida don naga kowa da kowa because i missed all of you too
much."
mahaifin nasa ya dan dafa kafadarsa tare da cewa
"we miss U too my son, shiga mota muje yau dai ka
dawo gida barrister Abbas."
da sauri mutum biyu dake tare da mahaifin nasa suka budewa masa kofa ya shige gaban motar
mahaifin nasa da sauran mutanen suka shige
motar a hankali direban ya juyar da motar tare da
ficewa daga airport din.
¤¤Unguwar NASSARAWA G.R.A¤¤
yanayin kyau da tsarin unguwar ne yasa komai dake ciki da kewayenta abin birgewa ne, ga duk
wanda yasanta zai bada lbrn kyawun gine-gine
dake cikinta ta yiwu sbd kasantuwarta ta masu
hannu da shuni.
A daya daga cikin gidajen wanda yaso ya zarta
sauran kyau da kawatuwa ma2ka ne motarsu abbas ta tsaya cak! Worn direban dake janta yayi
tafkeken gate din ya fara budewa a hnkl kuma
motar ta wuce izuwa ckn gdn.
*acan cikin gdn tsaye a cikin kyakykyawan kitchen
din gdn y'an mata ne guda biyu wadanda suka
shafe sama da awanni biyu suna hidima a cikinsa ba don komai ba sai don babban bakonsu dake
dawowa yau, bawai iya kitchen din kawai ba kaf
ilahirin gdn ya gauraye da kamshin girke-girken
alfarmar da kyawawan y'an matan biyu keyi.
Hira sukeyi jefi-jefi yayinda aikin nasu ke tafiya kai
da kai, byn kammala komai ne kuma suka fara aikin safarar abncn daga kitchen din izuwa wurin
da aka ware musamman don cin abnc, bisa wani
tafkeken tebiri wanda ke kewaye da kujeru.
A giftawar da suke ta falon ne wacce ke zaune ita
kadai ta dubesu gami da murmushi tace "lallai kuna
hidima sai kace masu saukar baki goma?? Mutum daya ne fa!!"
suka dakata daya daga cknsu tace "wlh momi nima
haka nace amma safiyya ce ta dage kinsan tana ji
da yayan nata."
wacce aka kira da safiyyar tace "momi kinga
laifina?? Yaya abbas ai daya ne tamkar da dubu bama goma ba."
duk sukai dariya, su biyun suka wuce tare da cgb
da shirya kayan dake kan faffadan tebirin.
"Zahra!"
safiya ta fadi sunan ba tare data dubeta ba tace "na
kagu naga yaya abbas kodon naga yadda ya canja a cikin shekaru ukun nan."
wanne canjawa zaiyi kuwa??
Yadda kika sanshi dai a haka zaki ganshi..
Sunma iso fa.
Zahra ta fada.
Safiyya tadan kasa kunne tare da cewa "nima naji alama."
*bayan dan kankanin lokaci sallamarsu ta ratsa
falon Abbas ne tare da abbansa wanda ke rike da
hannunsa, cak suka tsaya har yanzu abbas na rike
da doguwar jakarsa murmushi ne kawai ke tashi a
fuskarsa ga alama yana me farin ciki da dawowarsa gdn nasu.
A yanayin yadda farin ciki ke bayyana karara a
fuskokin dukkaninsu zaka fahimci yadda gdn ke
cike da soyayyar Abbas din daya shafe tsawon
shekaru uku yana karatu a kasar germany.
A hankali suka tako tare izuwa cikin falon, safiyya dake tsaye tana murmushi a hankali murmushin
nata kuma ya fara sauyawa izuwa bacin rai, ta zaro
ido gami da ja da baya a dan tsorace sakamakon
hade rai da yayan nata yayi dai-dai sanda suka
hada ido ya watsa mata ha
rara cike da tsana gami da jin haushinta....kuma???
Me hakan kenupi kenan..
Danjin wannan qayataccen labari...
Kasance da mu akodayaushe dan JOining din mu ko kuma
Title :
Zafin So Part 1
Description : Misalin karfe 12:00 na tsakar ranar wacce ke tsakiyar daukar zafi hamshakin katafaren jirgin saman nan kuma sananne wato TURKISH airli...
Rating :
5