Gwamnatin jihar Sokoto ta dauki alwashin hana bara a fadin jihar.
A cewar gwamnatin ta dauki wannan mataki ne dan magance matsalar talauci da kuma rashin aikin yi a jihar.
Alhaji Ahmad Aliyu shi ne mataimakin gwamnan jihar ta Sokoto kuma shi ne ya yiwa manema labarai karin haske dangane da lamarin.
Alhaji Ahmad ya ce, yanzu haka gwamnatin na bakin kokarinta dan samawa marasa abun yi kafin dokar ta fara aiki.
Ahmad ya kara da cewa wannan ce hanya daya tilo da za a bi dan cika alkawurran da gwamnatin jihar ta yi a lokacin yakin neman zabe dama matakin tarayya.
Title :
Za A Hana Bara A Jihar Sokoto
Description : Gwamnatin jihar Sokoto ta dauki alwashin hana bara a fadin jihar. A cewar gwamnatin ta dauki wannan mataki ne dan magance matsalar talauci...
Rating :
5