DAGA Rariya
A daren jiya Alhamis ne, rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, suka kaddamar da wani samame a wani gidan mai dake Kaduna, inda ake zargin matasa 'yan bumburutu ke cin kasuwar dare, inda suka tarwatsa gungun matasan tare da harbe daya daga cikinsu, wanda ake kyautata zaton shine jagoransu.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewar, lokacin da 'yan sandan suka dira sansanin 'yan bumburutun, sun yi ta harbi irin na kan mai uwa da wabi, inda matasan suka fasa da gudu, amma shi jagoran nasu mai suna Dan Aguro ya tsaya domin tattara jarkokin mansa, dalilin haka 'yan sandan suka bindige shi.
RARIYA ta halarci gidan iyayen matashin da aka kashe dake Unguwar Shanu Kaduna, inda ta tarar da cewar tuni an riga an yi jana'izar sa, yayin da jama'a ke amsar gaisuwar ta'aziyya.
Dukkanin kokarin da RARIYA ta yi domin jin bangaren rundunar 'yan sandan jihar ya ci tura, sakamakon rashin daukar waya da jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, ASP Zubairu Abubakar yake yi.
Title :
Yan Sandan Kaduna Sun Bindige Wani Matashi Dan Bunburutu Har Lahira A Garin Kaduna
Description : DAGA Rariya A daren jiya Alhamis ne, rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, suka kaddamar da wani samame a wani gidan mai dake Kaduna, in...
Rating :
5