Gogarman Kannywood, Ali Nuhu ya jawo hankalin masoyansa a duniya da su yi hankali da ‘yan damfara, ko kuma masu angulu-da-kan-zabo da sunansa a dandalin sadarwar zamani na ‘Soshiyal-Midiya’. Jarumin jaruman ya fadi hakan ne a yammacin yau, a yayin da ya sanya wasu hotuna har guda biyar wanda ke dauke da hirar da yayi da wata mai suna Hauwa S. Nma, a yayin da take sanar da shi wani labarin ban mamakin cewa sun yi hira da wani a maimakon shi Ali Nuhun.
Al’amarin dai, kamar LEADERSHIP HAUSA ta sansano, ya faru ne sanadiyar rasa wayarta da ta yi, a lokacin da ta samu wani wayar sai ta kasa samun abokanta na dandalin Shoshiyal-Midiya, wato a zauren ‘Faceebook,’ inda sai ta sake aikawa da gayyata don sadar da abota ga yawancin abokanta. Ta nan ne, a cewar Hauwa, ta samu wani shafi mai dauke da sunan Jarumi Ali Nuhu, inda har suka yi hira sosai. A hirar tasu ne, ta bayyana cewa jabun ‘Ali Nuhun’ ya yi mata wasu tambayoyi ta amsa daga nan ne ya yi mata albishir cewa ta ci wata babbar kyauta, ta musamman wai kasancewarta masoyiya ga jarumin.
Bayan samun wannan gagarumin albishir din ne Malama Hausa ta tuntubi jarumin a asalin shafinsa na sada zumunta na facebook mai suna Ali Nuhu Muhammed sabanin ‘Ali Nuhu’ kawai, wanda mutu zai iya ganin samfurin shafin bila-adadin a ‘Facebook’.
Wakilanmu sun tabbatar mana cewa a yayin da ta tuntubi jarumin ne, ya sanar da ita cewa shakka babu ‘yan damfara ne. Har ma ya kara da cewa shi dai bai taba tattaunawa da masoyansa a haka ba.
leadership Hausa
Title :
Yan Danfara Na Amfani Da Suna Ali Nuhu
Description : Gogarman Kannywood, Ali Nuhu ya jawo hankalin masoyansa a duniya da su yi hankali da ‘yan damfara, ko kuma masu angulu-da-kan-zabo da sunans...
Rating :
5