Wani matashi mai suna Safullahi Shehu ya tsallake rijya da baya, inda wasu y'an daba suka yi yunkurin hallaka shi a unguwar Dorayi dake karamar hukumar Gwale, jihar Kano, a ranar Lahadin da ta gabata.
Labarin ya samu ne jim kadan bayan aukuwar lamarin, inda wakilin mu ya zanta da shi a mazaunin sa dake unguwar Bello a Dorayi.
Matashin mai shekaru 28 ya bayyana cewa 'yan daban sun tare su ne a hanyar su ta zuwa unguwa tare da 'yan uwansa mata guda biyu, inda kwatsam suka ga mutum a gaban su yana ce musu ba hanya.
Safullahi ya kara da cewa yayin da ya bukaci ya ji dalilin hakan, sai wanda ya tare sun ya dake shi da makamin dake hannun sa yayin da sauran 'yan daban suka bayyana. Inda ba su yi wata-wata ba suka fara kai masa sara da wukake da addunan da suke dauke da su.
Hakan ta sa ya yi ta kokarin kare kan sa. Yayin haka ne mutanen dake kusa suka fara gudu zuwa gidajensu. Wani dan a dai-daita sahu ne ya kawo masa agaji, inda ya garzaya da shi ofishin 'yan sanda dake kusa, saboda bai sanar da shi inda yake da zama ba.
A nasu bangaren, 'yan sandan sun bayyana cewa za su kama tare da hukunta duk wanda suka tabbatar yana da hannu a cikin al-amarin.
A yanzu haka dai matashin yana gidan su dake Dorayi Karama don ci gaba da jinya sakamakon raunin da 'yan daban suka yi masa a ido, hannu da kuma bayansa.
Rariya
Title :
Yan Daba Sun Yi Yunkurin Halaka Wani Matashi A Kano
Description : Wani matashi mai suna Safullahi Shehu ya tsallake rijya da baya, inda wasu y'an daba suka yi yunkurin hallaka shi a unguwar Dorayi dake...
Rating :
5