A daren jiya Asabar ne wasu gungun matasa 'yan bindiga wadanda ba'a san ko su wanene ba, suka dira gidan wani ma'aikacin matatar man fetur ta Kaduna, mai suna Alhaji Yusuf Abdulkadir suka yi awon gaba dabshi a muhallinshi dake Rigachikum Kaduna.
Kamar yadda wani kanin Alhajin ya bayyana cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe goma na daren ranar Asabar din, lokacin da Alhajin yake kokarin shiga gidan na sa, lokacin ne motar wadannan matasa ta ja birki kusa da shi, kuma nan take suka sha gabansa tare da nuna masa bindiga, suka bukaci ya shiga motar ta su, ba tare da wani bata lokaci ba ya shiga, sannan suka figi hancin motar suka nufi hanyar Abuja.
RARIYA ta tuntunbi jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda dake Kaduna DSP Zubairu Abubakar dangane da wannan lamari, sai ya kada baki ya ce ba shi da labarin faruwar wannan lamari, amma zai tuntunbi DPO na Rigachikum, inda aka yi aika-aikar domin samun labari.
Saidai a wata zantawa da aka yi da wani abokin aikin Alhajin wanda ya bukaci da a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, yabce tun a daren jiya bayan faruwar lamarin suka sanar da ofishin 'yan sanda labarin.
Satar Alhaji Yusuf Abdulkadir ta zo 'yan kwanaki kadan ne, bayan rantsuwar da mataimakin shugaban rundunar 'yan sandan Nijeriya mai kula da shiyya ta 7, ASP Ballah Nasarawa ya yi, na shafe tarihin dukkanin wani tsagera a fadin jihar.
Rariya
Title :
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Ma'aikacin Matatar Man Fetur A Kaduna
Description : A daren jiya Asabar ne wasu gungun matasa 'yan bindiga wadanda ba'a san ko su wanene ba, suka dira gidan wani ma'aikacin matata...
Rating :
5