An fara samun ra'ayoyi da dama na jama'ar kasar nan akan rufe Majalisar Dattawa domin suna ganin cewa 'Yan Majalisar Dattawan sun dade suna kawo cikas ga ci gaban kasar nan.
Wasu daga cikin jama'ar sun nuna ra'ayoyin su akan cewa babu wani abu da 'Yan Majalisar Dattawan suke, illa kashe kudin talakawa. Sannan Kuma su ne makasudin wahalar da talakawa suke yi, domin ba su baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari hadin kai.
Wasu sun bada misali da kasar Senegal da suka rushe Majalisar Dattawa domin rashin kudi.
Masu karatu ko mene ne ra'ayinku game da wannan kira da wasu 'yan Nijeriya suka yi?
Title :
Wasu Al'ummar Nijeriya Sun Soma Kira Da A Rufe Majalisar Dattawa
Description : An fara samun ra'ayoyi da dama na jama'ar kasar nan akan rufe Majalisar Dattawa domin suna ganin cewa 'Yan Majalisar Dattawan s...
Rating :
5