Bisa nazarin yadda ake samun
yawaitar mace-macen aure
musamman a gidajen Hausa/Fulani,
yana da kyau a rika neman hanyoyin
magance su. So tari, idan har hakan ta
faru, a kan tankwashe kafa a fara
lissafin laifukan juna, alhali tun farkon
farawa an manta da bin hanya
madaidaiciya, yadda Manzon Rahama
(SAW) ya koyar.
A nazarin da aka gudanar, zawarawa
masu karancin shekaru sun yawaita a
mafi yawan manyan jihohinmu na
Arewa a yau. Zawarawa nawa ka sani
a unguwarku? Maza nawa ka sani,
wadanda suka saki matansu jim kadan
bayan aure? Wai shin me aka dauki
aure? Mene ne matsayin matarka a
gare ka? Me ya sa ake saurin dirka wa
mace saki bisa laifin da bai taka-kara
ya karya ba?
Wace irin huduba iyaye mata ke yi wa
‘ya’yansu ranar aure? Shin kwalliya na
biyan kudin sabulu ga iyaye masu
cewa ‘ya’yansu ‘Namiji ba dan goyo
ba’?
Wata uwa tagari, wadda ta san halin
zamantakewa ta yi wa diyarta
hudubar ABUBUWA 12, wadanda duk
diyar da ta rike za ta samu alheri a
rayuwarta na aure, kamar haka:
1 – Ki zama kamar baiwa ga mijinki,
sai shi ma ya zama kamar bawa a
gare ki.
2 – Kada ki nisance shi, sai ya manta
dake.
3 – Ki kiyaye masa hancinsa, jinsa, da
ganinsa; kada ya shaki wani abu daga
gare ki sai mai kamshi, kada ya ji wani
abu daga bakinki sai mai dadi, kada ya
ga wani abu daga gare ki sai mai kyau.
4 – Ki kiyaye masa lokacin abincinsa
da lokacin baccinsa, domin yunwa
tana hassala mutum, kuma gurbata
masa bacci na fusata shi.
5 – Ki kiyaye masa dukiyarsa, danginsa
da gidansa, domin suna da matukar
muhimmanci a gare shi.
6 – Ki guji yin farin ciki yayin da yake
cikin bacin rai, kuma ki kiyayi yin bakin
ciki, yayin da yake farin ciki.
7 – Ki girmama shi matuka shi ma zai
girmamaki matuka, fiye da yadda
kowa zai girmamaki.
8 – Ki sani cewa gwargwadon yadda
kike amincewa da ra’ayinsa
gwargwadon tausayawar da zai miki.
9 – Kada ki juya masa baya yayin da
ya kusanto gare ki.
10 – Ki sani baza ki sami yadda kike so
ba, har sai
kin zabi yardarsa a kan yardarki, kin
fifita son ransa a kan son ranki.
11 – Kada ki fiya naci ko fushi a
lokacin da kike neman wani abu a
gare shi, sai ya kosa dake.
12 – Daga karshe don girman, Allah ki
yi hakuri, ki zamo shimfida ga mijinki
zai zamo rumfa a gare ki….
Ya ku masu karatu musamman iyaye
mata, wace hudubar ku ke yi wa
‘ya’yanku ranar aure?
Title :
Wacce Irin Nasiha Kike Wa Yar Ki Lokacin Aurenta
Description : Bisa nazarin yadda ake samun yawaitar mace-macen aure musamman a gidajen Hausa/Fulani, yana da kyau a rika neman hanyoyin magance su. So...
Rating :
5