Lauya dake kare 'Yan Shi'a a rikicin daya faru tsakanin rundunar Sojojin Nijeriya da 'Yan Shi'a, Barista Maxwell Kyon, ya fito fili ya bayyana gaskiyar yanayin lafiyar Zazzaky da matarshi Zeenatu a inda suke tsare a hukumar tsaro ta kasa dake Abuja.
Barista Kyon ya bayyana hakan ne, lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, a yayin wani taron manema labarai da Kungiyar Lauyoyi dake kare 'Yan Shi'a karkashin jagorancin Lauya Festus Okoye suka kira a cibiyar 'yan jaridu dake Kaduna.
Barista Kyon ya cigaba da cewar yana daya daga cikin tawagar da suka samu ganawa da Zakzaky da matarshi a ranar daya ga watan Afirilu na wannan shekarar, inda yace ga dukkanin wanda ya san Zakzaky a baya, to ba zai iya shaida shi a halin yanzu ba, sakamakon fita hayyaci da Malamin ya yi, ya rame matuka kuma baya iya tafiya akan kafafuwanshi, yana dingishi ne sannan baya gani sosai.
Lauyan 'Yan Shi'an ya cigaba da cewar sun tsorata matuka da suka ganshi a wannan yanayi, matarshi Zeenatu itace ta bayyana mishi cewa Lauyoyin dake kare kane suka zo ganinka, sannan suka samu daman tattaunawa da shi.
Lauya Kyon ya tabbatar da cewar Malamin ya rasa idonshi na hagu, sannan ya samu munmunan rauni a hannun shi na hagu wanda zai yi wuya ya cigaba da amfani dashi, sannan idonshi na dama yana cikin wani yanayi mai tada hankali, yayin da kafarshi ta hagu da kyar yake motsa ta, sannan bangaren matarshi Zeenatu tana jinyar munmunan raunin data samu a ciki sakamakon harbinta har sau uku da akayi a ciki, sannan aka ajiyeta na kwanaki a Asibitin 44 dake Kaduna ba tare da wata kulawa ba.
Tun farko da yake gabatar da jawabi Lauya Festus Okoye, yace duniya ta shaida a halin yanzu cewa Sojin Nijeriya sun shirga karya, lokacin da sukace sun kashe mutum 7 ne kawai, sai gashi gwamnatin Kaduna ta tabbatar da turbude gawawwakin 'Yan Shi'a 347 a rami guda.
Title :
Sheikh El Zakzaky Da Zeenatu Suna Cikin Mawuyacin Hali - Barista Maxwell Kyon
Description : Lauya dake kare 'Yan Shi'a a rikicin daya faru tsakanin rundunar Sojojin Nijeriya da 'Yan Shi'a, Barista Maxwell Kyon, ya fi...
Rating :
5