A safiyar jiya Alhamis ne dakarun sojojin Nijeriya na 'Opration Lafiya Dole' suka yi nasarar cafke wasu shugabannin kugiyar Boko Haram.
Sojojin sun kama jagororin 'yan ta'addan ne har su shida a garin Kala Balge sakamakon matsa musu lamba da sojojin suka yi a dajin Sambisa.
Wadanda aka kama din sune Musa Kalile Sabakara (Amir), Babagana John (dan leken asiri kuma mai sayar musu da kayan abinci), Isah Abakar (Amir) da Usman Abasa, (wanda ya kware wajen satar shanu da kuma sayar musu da kayan abinci ), sai kuma Bukar Gujja (wanda shi kuma tela ne mai dinkawa 'yan ta'addan kaya) da Bukar Kahalifa (shi ma telan 'yan Boko Haram din ne), inda kuma yanzu haka ana kan gudanar da bincike a kansu
Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin kakakin rundunar sojojin, Kanel Sani Kukasheka Usman.
Title :
Photos: Sojoji Sun Kama Wasu Shugabannin Boko Haram
Description : A safiyar jiya Alhamis ne dakarun sojojin Nijeriya na 'Opration Lafiya Dole' suka yi nasarar cafke wasu shugabannin kugiyar Boko Ha...
Rating :
5