Majalisar dokokin jihar Nassarawa ta tsige membobinta shida wadanda ta dakatar da su a makon jiya daga shugabancin wasu daga cikin kwamitocinta.
Kakakin majalisar, Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi ne ya sanar da hakan a garin Lafia bayan wani zama da majalisar ta yi a jiya, inda 'yan majalisar suka yi na'am da salon shugabancin kakakin nasu.
Alhaji Balarabe Abdullahi ya ce an yanke shawarar tsige 'yan majlaisar da aka dakatar da su daga shugabancin komitocin ne bayan wani taron ya'yan jam'iyyar APC dake majalisar kafin sannan aka gabatar da batun gaban majalisar.
Kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawan yace 'yan majalisar shida sun nuna halin rashin da'a tare da tayar da zaune tsaye majalisar saboda haka ne aka dauki wannan mataki akan su.
Su dai 'yan majalisar guda shida wadanda suka hadar da Kasim Muhammad Kasim mai wakiltar Akwanga ta kudu, Murtala Sodangi mai wakiltar Nassarawa ta tsakiya, Mohammed Okpoku mai wakiltar mazabar Udege da Loko, Musa Ali Scatter mai wkiltar Keffi ta gabas, Makpa Malla na mazabar Wamba da kuma Abubakar Kana na mazabar Kokona ta yamma, sun ki amincewa da nadin kantomomi na a majalisun kananan hukumomi goma sha daya cikin goma sha uku dake jihar kafin a gudanar da gwamnan jihar Umar Tanko Almakura ya yi kafin a gudanar da zabe. 'Yan majalisar sun ce yin hakan ya sabawa doka.
Sources Rariya
Title :
Majalisar Jihar Nassarawa Ta Tsige Membobinta Guda Shida
Description : Majalisar dokokin jihar Nassarawa ta tsige membobinta shida wadanda ta dakatar da su a makon jiya daga shugabancin wasu daga cikin kwamitoc...
Rating :
5