A kwanakin baya ne wasu hotunan
fitaccen jarumin finafinan Hausa Sani
Musa Danja suka yi ta yawo a gari, inda
aka nuno shi jina-jina, zaune a gaban
sojoji da bindiga, wanda hakan ya sa aka
yi ta fassara hotunan ta fuskoki daban-
daban.
Fassarar da aka fi yi wa hotunan shi ne,
sojoji sun kama Sani Danja da kan jariri a
bayan motarsa, inda har ta kai ga sun yi
masa dukan kawo wuka, sannan kuma
yana tsare a hannun hukuma. Hakan ne
ya sa wakilinmu ya nemi jin ta bakin
jarumin don tabbatar da gaskiyar lamarin.
Sani Danja ya ce, “Wannan hoto da ake ta
yadawa ba komai ba ne, illa sharin
makiya da mahassada ne saboda kawai
su bata min suna. An dauki hotunan ne a
yayin da muke shirya wani fim din
Turanci a jihar Delta, mai suna ‘Behind
The Will.’
Shi dai wannan fim an yi shi ne kan
yadda ake satar danyen mai da sauran
al’amuran da suka jibanci harkar
ta’addanci a yankin Neja-Delta, amma sai
ga shi an juya shi da wata manufa
daban”. Sani Danja ya kara da cewa
al’ada ce na kowane fim idan ana kan
daukarsa sai an yi hotunan ko dan
saboda kada a manta wasu wuraren,
wanda dalili kenan da aka dauki wannan
hoto, da kuma irin nuna kwarewa da shi
mai kwalliyar ya yi, shi ya taimaka wajen
daukar hoton da aka yi, domin duk wanda
ya ga yadda aka yi wa fuskarsa, spzai
dauka jini gaske ne ya malale masa
fuska.
Ya kara da cewa kazafin da aka yi masa
ya yi armashi ne ta yadda mahadsadansa
suka yi ta yada hotunan tare da fassara
su da manufofi daban-daban, domin shi
kansa ya yi mamaki a lokacin da ya ji
jama’a na ta kiransa don jin gaskiyar
lamarin.
Game da dalilin da ya sa aka rage ganin
fuskarsa a finafinan Hausa kuma, Sani ya
ce ya rage ne saboda uzurorin da suke
gabansa, sannan kuma lokaci ne da ya
kamata a ce ya rage fita a finafinai
barkatai, mudamman wadanda ba sunda
ma’ana.
Don haka ba kowane irin fim za a yi
tsammanin za a dinga ganinsa a ciki ba.
Haka kuma Sani ya ce saba ganinsa da
amininsa Yakubu Mohammed a koda
yaushe da ake yi, ya dan ragu ne
sakamakon auren da kowannen su ya yi,
inda ya ce babu yadda za a yi a hada
rayuwar lokacin da muke yake da aure da
kuma lokacin da ba shi da aure.
Sannan kuma yana ayyukansa ya taimaka
wajen rage karfin dangatarsa da aminin
nasa, saboda a wasu lokutan yanayin aiki
ke sa su dau tsawon lokaci ba su hadu
ba.
Title :
Mahassada Ne Ke Neman Bata Mini Suna - Sani Danja
Description : A kwanakin baya ne wasu hotunan fitaccen jarumin finafinan Hausa Sani Musa Danja suka yi ta yawo a gari, inda aka nuno shi jina-jina, za...
Rating :
5