Zakzaky ya bada umarnin a wa lt. Gen. Ty buratai tare-tare a zaria, wanda hakan ka iya bawa 'yanta'adda damar su hallaka shi, bayan allah ya tsallakar da shi wannan kaidin, su dai mabiya zakzakin kuma suka yi yunqurin hallaka shi, nan ma allah ya tsallakar da shi, wanda a qarshe yaqi ya nemi ya barqe tsakanin rundunar sojojin nigeria da 'yan shi'a, allah cikin hikima da rahamarsa ya bawa rundunar sojojin nigeria nasara a kan su, suka damqe zakzakin kuma suka tsira da rayukansu in banda wasu sojoji da aka jikkata ko aka kashe.
Duk mai hankali da sanin yakamata ya sani fa sarai wannan ba wai rigima ba ce tsakanin buratai da 'yan shi'a; rigima ce tsakanin nigeria da 'yan shi'a, kuma nasarar da aka samu ba wai buratai ne a matsayin sa na buratai ya samu ba, nigeria ce ta samu, don haka duk mai kishin qasa ya gamsu cewa cafke zakzakiy maslahar qasa ce kuma ci gaba da tsare shi adalci ne kuma sakin sa barazana ne ga hadin kai da zaman lafiyar qasa ne.
Don haka kiran a saki zakzakiy rashin kishin qasane wanda kuma ba za a lamunta ba.
Allah ya ba mu zaman lafiya a nigeria ya mana maganin duk mai son tada fitina.
Title :
Kiran A Saki Zakzakiy Rashin Kishin Qasa Ne - Baban Hamda
Description : Zakzaky ya bada umarnin a wa lt. Gen. Ty buratai tare-tare a zaria, wanda hakan ka iya bawa 'yanta'adda damar su hallaka shi, bayan ...
Rating :
5