An shiga shakku a jihar Nassarawa sakamakon rashin sanin takamaiman inda gwamnan jihar Umaru Tanko Al-Makura ya shiga, wanda ya bar jihar kusan mako guda kenan ba tare da ya bada sanarwar inda zai je ba.
Wata majiya daga fadar gwamnatin jihar ta bayyana cewa gwamnan ya shilla kasar waje ne kan wasu bukatun kansa, kuma ya ki bada sanarwar tafiyarsa don kada ya baiwa mataimakinsa, Silas Agara rikon kwarya.
Bincike ya nuna cewa akwai rashin jituwa tsakanin gwamnan da mataimakinsa, wanda na hannun daman tsohon gwamnan jihar Sanata Abdullahi Adamu ne. Wasu na ganin cewa rashin baiwa mataimakin nasa rikon kwaryar da gwamnan ya yi, ba ta rasa nasaba da hakan.
Bincike ya nuna cewa rashin gwamnan a jihar na neman jefa al'ummar jihar cikin mawuyacin hali sakamakon yadda al'amura suka tsyaya cak a jihar.
Har dai zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wani daga cikin mukarraban gwamnan da ya bada haske kan bulaguron da gwamnan ya yi, wanda hakan ya jefa al'ummar jihar cikin shakku na rashin sanin takamaiman inda gwamnan nasu yake.
Title :
Jihar Nassarawa Na Cigiyar Gwamnansu
Description : An shiga shakku a jihar Nassarawa sakamakon rashin sanin takamaiman inda gwamnan jihar Umaru Tanko Al-Makura ya shiga, wanda ya bar jihar ...
Rating :
5